✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kabilar Ibo suna so su girbi abin da ba su shuka ba

Tun da Shugaba Muhammadu Buhari ya fara takarar neman Shugabncin Kasa a  shekarar 2003, har ya kai ga cin zabe a  2015, kabilar Ibo na…

Tun da Shugaba Muhammadu Buhari ya fara takarar neman Shugabncin Kasa a  shekarar 2003, har ya kai ga cin zabe a  2015, kabilar Ibo na Shiyyar Kudu maso Gabas da ta kunshi jihohin Imo da Anambra da Abiya da Enugu da Ebonyi ba su taba goyon bayansa ba, amma kuma suna ta kokawa da gwamnatinsa a kan ta maida su saniyar ware ba a damawa da su balle a sha tare da su a cikin gwamnatinsa.

Zargin haka ba ya rasa nasaba da irin yadda kila suke ganin an dama kuma an sha da su a shekara 16 da gwamnatin PDP ta yi a karagar mulkin kasar nan.

Alal misali a tsawon mulkin Jam’iyyar PDP, ’yan kabilar Ibo su ke rike da mukami na uku na zababbun kasar nan, wato Shugaban Majalisar Dattawa.

Tashin farko a gwamnatin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo Sanata Eban Eweram, shi aka fara zaba a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa. Sai Sanata Chuba Okadigbo, bayan shi sai Sanata Anyim Pius Anyim daga shekarar 2000 zuwa 2003, sai Sanata Adolphus Wabara daga 2003 zuwa 2005, Sanata Ken Nnamani 2005 zuwa 2007, dukkansu sun shugabanci Majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar PDP. Duk da cewa a lokacin Shugaba Obasanjo, ya rika nada-sauke ga shugabannin Majalisar Dattawan duk lokacin da ta raya masa, tamkar canja riga.

A shekarar 2007 da marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa daga Arewa maso Yamma ya zama Shugaban Kasa, Dokta Goodluck Ebele Jonathan daga Kudu maso Kudu ya zame masa Mataimaki, sai kuma Shugabancin Majalisar Dattawa ya dawo Arewa ta Tsakiya, inda ya fada hannun Sanata Dabid Mark, wanda ya rike wannan mukami tun daga shekarar 2007 zuwa 2015, tsawon shekara 8.

Mai karatu kada ka manta, bisa ga irin rawar da ’yan kabilar Ibo suka rika takawa wajen samun nasarar PDP a zabubbukan, ya sanya har shugabantar jam’iyyar a kasa baki daya dansu Yarima Bincent ya yi. Kazalika har Sakataren Gwamnatin Tarayya dan kabilar Ibo ya yi, wato Sanata Anyim Pius Anyim, bisa ga irin yadda kusan dukkansu suke cikin Jam’iyyar PDP.

A maganar da ake yi a yau dukkan gwamnonin jihohin kabilar Ibo biyar ’yan Jam’iyyar PDP ne, haka labarin yake kan akasarin majalisun dokokinsu na kasa da jihohi. Duk da karin kuri’un da mutanen jihohin biyar suka kada wa Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC a zaben bana da ya kai dubu 403 da 968, idan aka kwatanta da dubu 198 da 248 da suka kada masa a zaben 2015, da za a iya cewa sun dan cirza, samuwar haka ba zai zama dalilian da za su sa ’yan kabilar Ibo su rika kururuwar lallai sai an yi da su a cikin wannan gwamnati ba.

Babban burin da ke gaban kabilar Ibo bai wuce yadda za su samu shugabancin kasar nan a zaben shekarar  2023 ba, in Allah Ya kai mu. Amma kuma ba wai masu kula da yadda harkokin siyasar kasar suke gudana ba, a’a, hatta daga cikinsu (kabilar Ibon), akwai masu kallon irin wadancan mutane, tamkar sun rude ne.

Alal misali dattijo Cif Mbazulike Amechi mai shekara 92 kuma daya daga cikin ’yan ga-ni-kashe-nin tafiyar siyasar tsohon Shugaban Kasa a Jamhuriyya ta Daya, Dokta Nnamdi Azikwe na Jam’iyyar NCNC a tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust Sunday ta ranar 22 ga Yunin da ya gabata ya yi tambaya ga ’yan kabilar Ibo cewa, “Don me ’yan kabilar Ibo suke son su kutsa kai, su kuma zama cikin na gaba-gaba a gwamnatin APC da ba su yi wa aikin komai ba?” Ya ci gaba da cewa “Bai kamata ba a wannan lokaci ’yan kabilar Ibo su rika rokon a ba su mukamai a wannan gwamnati, maimakon haka ya kamata su kara daura damara da tuntuba da tattaunawa kan yadda dan kabilar Ibo zai zama Shugaban Kasa ne a shekarar 2023.”

A zaman fatar a yi da su, ’yan kabilar Ibo sun baza jita-jitar cewa gwamnatin Buhari za ta nada dansu kuma tsohon Minista a gwamnatin, Cif  Ogbonaya Onu a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya, don a tafi da su a gwamnatin. Amma wannan fata tasu ta zama mafarki, saboda Shugaba Buhari ya sake nada Mista Boss Mustapha daga Jihar Adamawa a Arewa maso Gabas a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya karo na biyu.

Idan aka koma baya, a cikin mukaman da aka raba a shugabancin Majalisar Dokoki ta kasa, za a ga  tsohon Gwamnan Jihar Abiya Dokta Orji Uzor Kalu (APC, Abiya) shi kadai ya samu shiga cikin shugabannin Majalisar Dattawan a matsayin Gagarabadan Majalisar, yayin da a Majalisar Wakilai, dan Majalisa Tony Okechukwu (PDP, Enugu), ya zama Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye. Wadannan zababbu biyu su kadai ne masu rike da wasu manyan mukamai a majalisun dokokin na kasa guda biyu.

Duk da barranta da ’yan kabilar Ibo suka yi wa Jam’iyyar APC, kamar yadda dattawansu irin su Cif Amechi suke nuna mUsu, amma da yake an ce mara kunya shi ke cin tuwon gidan biki, har ya nemi a kara masa miya, sai ga shi wadansu daga cikinsu da kungiyoyinsu irin su na tabbatar da kafuwar kasar Biyafara da ta Ohanaeze Ndigbo, sun dage a kan lallai sai a yi da su a wannan gwamnati. Sannan a shekarar 2023, a dauki Shugabancin Kasar nan a mika musu.

An yi sa’a a cikinsu akwai dattawa irin su Cif Amechi da suka san yadda aka yi tafiyar mulkin kasar nan tun daga Jamhuriya ta Daya da ta Biyu, har zuwa yanzu da sukan gaya masu gaskiyar al’amari.

Kamar yadda Shugaba Buhari ya fada wa ’yan kabilar Ibo a lokacin da ya kai rangadin gangagamin neman zaben bana a hiyyar, cewa ya yi shugabancin kasar nan, batu ne na a tattauna.

A tawa fahimtar ita tattaunawa a cikin lumana da kwanciyar hankali da hakuri da juna ake yin ta har kowa ya samu biyan bukata, amma ba ta barazana da neman ta da husuma ba, kamar yadda shugabannin kabilar Ibo suka bar matasansu suke ta kada kugen yaki da neman ballewa a karkashin kungiyarsu ta neman tabbatar da kasar Biyafara da ta Ohaknaeze Ndigbo ba.

A ganina yadda a kullum mulkin dimokuradiyyar kasar nan yake kara kankama, lokaci ya wuce da wata kabila daga cikin manyan kabilun kasar nan uku (Ibo, Hausa da Yuroba) za ta yi ta kamfen din bata suna da cin mutuncin wata kabila ta kuma samu mulki a bagas.

Daya daga cikin dalilan da suka sanya Sanata Rochas Okoracha tsohon Gwamnan Jihar Imo a 2014, ya bar jam’iyyarsu ta APGA zuwa APC, bai wuce yadda dan kabilar Ibo zai samu zama Shugaban Kasar nan a shekarar 2023 ba, muradin da ya yi kamfen a kai, amma ’yan kabilarsa suka yi biris da shi, har kawo yanzu da yake shaida masu su sake lale.