✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kabilun Barbar sun toshe bututun iskar gas a Libya

kungiyar masu fafutikar hakkin auzinawan Libya sun fasa bututun da ke kai iskar gas zuwa tashoshin lantarkin kasar, inda suke bukatar a samar musu ’yan…

Kabilun Amazigh Barbar na zanga-zanga a gaban ofishin Firayiministan Libyakungiyar masu fafutikar hakkin auzinawan Libya sun fasa bututun da ke kai iskar gas zuwa tashoshin lantarkin kasar, inda suke bukatar a samar musu ’yan bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda wani jami’in gwamnati ya bayyana.
“Bututun iskar gas din mai tsawon kilomita 50 da ke garin Nalout an toshe shi, inda tsofafin ’yan tawayen Berber daga yankin Jebel Nafussa suka fasa shi,” inji Salah al-Gharada, shugaban majalisar kabilun yankin, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.
Gharada ya ce masu fafutikar ’yanci, wadanda suka fafata yaki wajen kawar da Moa’amer Ghaddafi a shekarar 2011, suna kira kan lallai a kara fadada ’yanci da walwala a garesu, bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki a nan gaba.
kabilun Barbar da Tubu da Tuareg, ’yan tsirari ne wadanda ke da kujeru shida daga cikin kujeru 60 na majalisar kasar, don haka suke bukatar a samar da sabon kundin tsarin mulki, inda za a samar da ’yancinsu bisa la’akari da harsunansu da al’adunsu da hakkokin kabilun.
kabilun Barbar sun kai kashi 10 cikin 100 na yawan al’ummar Libya. Sun sha wahala, an azabtar da su a zamanin mulkin Ghaddafi, don haka suke jin cewa an tauye su, a wannan sabuwar gwamnati, wadda suka bayar da muhimmiyar udunmuwa wajen tayar da kayar baya, don ganin kafuwarta. A watan Yulin bara suka janye wakilansu daga majalisar kasa, don nuna fushinsu kan yadda aka tauye musu hakki.
Sun yi alwashin kin biyayya ga hukuma, don tursasa majalisar kasa ta biya musu bukatunsu. Don haka kabilun Barbar da ke Nalout suka kule bututun da ke samar da iskar gas ga tashar lantarkin Millitah. A cikin Satumbar bana sun kawo cikas ga bunkatar tattalin arzikin kasar, al’amarin da ya haifar da ake hako man da yawansa bai kai ganganr burbataccen man fetur dubu 100 ba.