✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kabilun kudancin Kaduna sun karyata sanarwar ‘yan sanda

Kungiyar kabilun kudancin Kaduna da aka fi sani da SOKAPU ta ce babu kashin gaskiya a sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta fitar…

Kungiyar kabilun kudancin Kaduna da aka fi sani da SOKAPU ta ce babu kashin gaskiya a sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta fitar da ke dauke  da sa hannun Kakakinta, ASP Muhammed Jalige a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar CP MM Muri.
Sanarwar rundunar ‘yan sandan da  ta musanta kashe-kashen da shugaban kungiyar Cigaban kabilar Adara, Awemi Dio Maisamari ya fitar inda ya ke bayyana kashe-kashen da ‘yan bindiga su ka yiwa jama’arsu.
Sanarwar ta ce rundunar ‘yan sandan na koqarin kawar da hankalin mutane ne domin babu kashin gaskiya a sanarwar da suka fitar.
Yace kungiyar cigaban kabilar Adara ta sanar da mutuwar mutane 20 da aka yi musu kisan gilla bayan rikicin da aka yi a Gonan Rogo da Makyalli da Unguwan Rana da ke karamar hukumar Kajuru na ranakun 13 da 14 na watan Mayun bana.
“Duk da cewa a sanarwar rundunar ‘yan sandan sun tabbatar da kisan mutane 27 yayin da aka kai hari a wadannan garuruwan.
“Amma kuma sun karyata sake kai wasu hare-haren a dukkanin fadin karamar hukumar bayan nan.
“Hakan yasa rundunar ta gargadi duk wasu masu yada labaran bogi, tare da gargadin ‘yan jarida illar da irin wadannan labaran zai haifar.” In ji sanarwar
Takardar tace bayan bayyanar sanarwar rundunar ‘yan sandan ne kungiyar SOKAPU karkahin jagorancin shugaban ta Jonathan Asake suka kai ziyarar gani da ido a kauyukan da aka kai hare-haren, inda su ka ce babu wata takarda da shugaban Adara, Dio Maisamari ya fitar a ranar 28 ga watan Mayu wanda ‘yan sandan ke karyatawa.
 kuma yace sun samu labarai masu tayar da hankali daga jama’ar kauyen da abin ya shafa.
Har ila yau, a cikin takardar tasu, SOKAPU ta kuma zargi Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmed El-Rufa’i da rashin fitowa fili yayi Allah wadai da hare-haren Kajuru da aka faro shi tun bara, ballantana ya tallafa musu da wani abu.
“Don haka mu ke ganin akwai wata makarkashiya da ta sa rundunar ‘yan sandan jihar ta fito da nata sanarwar domin  musanta kai wadancan sabbin hare-haren.”
A karshe kungiyar ta SOKAPU ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi kokarin samar da rundunar  sojojin da ta samar a jijohin Sokoto da Katsina da ke fafatwa da ‘yan binda da a samar da su a sassan jihar Kaduna, sannan tayi kira ga kungiyoyin Tarayyar Turai da Kotun da ke hukunta manyan laifuffuka ta Duniya da kungiyar kare haqqin bil’Adama ta Amnesty International da kuma Majalisar dinkin Duniya da su gaggauta sa baki a lamarin tare da kawo musu dauki.