Da Dumi Dumi

Kabilun Najeriya (1)

A wannan mako Aminiya ta yi nazari da bincike kan yawan kabilun da suke Najeria. Lura da cewa a makon jiya ne kasar nan ta cika shekara 59 da samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka shafin Adabi yana taya ’yan Najeriya murna. Najeriya tana da ƙabilu daban-daban masu yawa waɗanda suka bambanta ta fuskoki da dama da suka haɗa da harshe, al’ada, wurin zama da kuma addini da sauransu. Zuwa yanzu, akwai ƙabilu da aka san da zamansu har guda 402 da biyu da Rumbun Ilimi ya tattara kamar yadda yake wallafe a shafinsa na Intanet. Kowace Ƙabila an rubuta jiha ko jihohin da ake iya samun ta a ciki:

 

Jerin sunayen kabilun Najeriya da jihohin da ake samunsu

 1. Abayon, ana samunsu a Jihar Kuros Riba.
 2. Abua (Odual), ana samunsu a JIhar Ribas.
 3. Achipa (Achipawa), ana samunsu a Jihar Kebbi.
 4. Adim, ana samunsu a Jihar Kuros Riba.
 5. Adun, ana samunsu a Jihar Kuros Riba.
 6. Afenmai, ana samunsu a Jihar Edo,
 7. Affade, ana samunsu a Jihar Yobe.
 8. Afikpo, ana samunsu a Jihar Ebonyi.
 9. Afizere, ana samunsu a Jihar Filato.
 10. Afo, ana samunsu a Jihar Filato.
 11. Agatu, ana samunsu a Nasarawa da Benuwai.
 12. Agbo, ana samunsu a Jihar Kuros Riba.
 13. Aha, ana samunsu a Jihar Neja.
 14. Akaju-Ndem (Akajuk), ana samunsu a Jihar Kuros Riba.
 15. Akoko, ana samunsu a jihohin Edo da Ogun.
 16. Akweya-Yachi, ana samun su a Jihar Benuwai.
 17. Akyekuru, ana samunsu a Jihar Nasarawa.
 18. Alago, ana samunsu a jihohin Nasarawa da Filato.
 19. Amo, ana samunsu a Jihar Filato.
 20. Anaguta, ana samun su a Jihar Filato.
 21. Anang, ana samunsu a Jihar Akwa Ibom.
 22. Adoni, ana samunsu a jihohin Akwa Ibom da Ribas.
 23. Aho (Afo), ana samunsu a jihohin Benuwai da Nasarawa.
 24. Angas, ana samunsu a jihohin Bauchi, Jigawa da Filato.
 25. Ankwei (Goemai), ana samunsu a jihohin Nasarawa da Filato.
 26. Anyima, ana samunsu a Jihar Kuros Riba.
 27. Anyishi, ana samunsu a Jihar Benuwai.
 28. Arochukwu (Abiriba), ana samunsu a Jihar Abiya.
 29. Attakar (Ataka), ana samunsu a Jihar Kaduna.
 30. Ashe (Koro-Ala), ana samunsu a Jihar Filato.
 31. Auyoka (Auyakawa), ana samunsu a Jihar Jigawa.
 32. Awori, ana samunsu a jihohin Legas da Ogun.
 33. Ayu, ana samunsu a Jihar Kaduna.

34.Ɓachama (Ɓashama/Ɓacama), ana samunsu a Jihar Adamawa.

 1. Baban (Babar), ana samunsu a Jihar Adamawa.
 2. Bachere, ana samunsu a Jihar Kuros Riba.
 3. Bakulung, ana samunsu a Jihar Taraba.
 4. Bada, ana samunsu a Jihar Filato.
 5. Bade, ana samunsu a Jihar Yobe.
 6. Bahumono, ana samunsu a Jihar Kuros Riba.
 7. Bakulung, ana samunsu a Jihar Taraba.
 8. Balankuk, ana samunsu a Jihar Filato.
 9. Bli, ana samunsu a Jihar Taraba.
 10. Bambora (Bambarawa), ana samunsu a Jihar Bauchi.
 11. Bambuko ana samunsu a Jihar Taraba.
 12. Banda (Bandawa), ana samunsu a Jihar Taraba.
 13. Banka (Bankawa), ana samunsu a Jihar Bauchi.
 14. Banso (Panso), ana samunsu a Jihar Adamawa.
 15. Banu, ana samunsu a Jihar Adamawa.
 16. Bara (Barawa), ana samunsu a Jihar Bauchi.
 17. Barke, ana samunsu a Jihar Bauchi.
 18. Baruba (Barba), ana samunsu a Jihar Neja.
 19. Bashiri, ana samunsu a Jihar Filato.
 20. Bassa-Nge, ana samunsu a jihohin Kaduna, Kogi, Neja da Filato.
 21. Bassa-Komo, ana samunsu a Jihar Kogi.
 22. Batta, ana samunsu a Jihar Adamawa.
 23. Baushi, ana samunsu a Jihar Neja.
 24. Baya, ana samunsu a Jihar Adamawa.
 25. Bakwara, ana samunsu a

Mun ciro wannan bincike ne  daga Rumbun Ilimi da kuma littafin Ajaegbu H.I., ST. Matthew-Daniel B.J., and Uya O.E. (2000). Nigeria A people United, A Feature Assured Bolume 1, A Compendium, Millenium Edition. Gabumo Publishing Company Limited, Nigeria.

ADVERTISEMENT

Za mu ci gaba

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya