✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada a kara harajin kayayyakin bukatu (BAT)

Daga cikin tsare tsaren da aka aiwatar a watan Janairun bana ne, taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ya amince da karin kudin harajin kayyayakin bukatun…

Daga cikin tsare tsaren da aka aiwatar a watan Janairun bana ne, taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ya amince da karin kudin harajin kayyayakin bukatun yau da kullum (BAT) daga kashi 5 zuwa kashi 7.5, wanda hakan ya nuna an yi karin kashi 50 ke nan.

Ministar Kudi da Kasafi da kuma Tsare-Tsare Zainab Ahmad ta bayyana haka a wajen wani taro da aka gudanar na kungiyoyin farar hula da sauran hukumomin kan daftarin kudirin shekarar 2020 zuwa 2022 na tsarin tabbatar da bunkasar cimma tasirin ci gaban kasa.

Ministar ta ce karin kudin harajin ya fado ne bisa tsarin bunkasar ci gaban kudaden shiga, wanda shi ne ginshikin habaka ci gaban gwamnati, baya ga sauran wasu hanyoyi na sayar da kadarorin gwamnati da sauran al’amuran da ba su shafi harkar man fetur ba, da kuma matsawa daga tsarin nan na sayar da hannayen jari da samar da rance. Sai dai fa wannan karin na iya zama ne, idan har ya samu amincewar Majalisar Dokoki ta Kasa, wanda na daga cikin tsarin bin ainihin shirin da kwamiti na mussaman da Shugaban Kasa ya kafa wanda ya kunshi manyan jami’an gwamnati da kuma na masu zaman kansu da ke karkashin ikon Bismack Rewane na Hukumar bin Kididdigar Tattalin Arzikin Kasa a matsayi Shugaba.

A cewar Malama Zainab, gwamnati za ta tabbatar da kudin harajin zai fito ne daga karin kudaden shigar da za ta samar, wanda ya kasance abu mai nauyi da take fuskanta ta wajen al’amuran cikin gida da kuma basussukan kasashen waje, hada da sauke hakkinta na bunkasa tattalin arzikin kasa, An samu kudin harajin da ya tasam ma  Naira biliyan 900 a cikin shekara 6 da suka shige, wanda ake tsammanin hakan kan iya bunkasa, har ya kai zuwa Naira tiriliyan 1.35 a shekara. Hakazalika gwamnati ta yi karin kudin harajin ne ganin harajin da ake karba a kasar nan shi ne mafi karaci idan an kwatanta da sauran kasashen Afirka.

Ganin yadda gwamnati take bukatar karin kudade, baya ga irin kalubalen da ke gabanta, karin kudin harajin ya kasance wani abu mai wahala gare ta, wannan lamari ya jawo suka da cece-kuce daga bangarori daban-daban, irin su Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masana’antu, Ayyukan Gona da Ma’adinai ta Kasa da Kungiyar Masu Masuna’antu ta Kasa da  gamayyar kungiyoyin ma’aikata da da sauransu. Wannan wakilci na gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu sun yi magana da murya daya inda suka yi kiran a sake duba tsarin, wanda idan aka kaddamar da shi kan iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin da durkusar da harkar masana’antu.

Harajin zai zama tamkar komai ka taba ya shafe shi, kama daga sayen kayan da za a sarrafa har zuwa ya kasance abin amfani ga al’umma, kai har ta kai ga karamin mutum mai sayen kayan a shago, don haka mai sayen kayan shi ne biyan harajin ya fi shafa. Hakazalika masana’antu kan iya samun koma baya a kan karin harajin, don dole su takaita kayyaykin da suke sarrafawa, wanda a yanzu ba shi ne abin da tattalin arzikin kasar nan yake bukata ba.

Shi kansa karin kudin harajin kan iya ta’azzara tashin gwaron zabo kan kayyayakin yau da kullum, wanda lamarin kan koma ga mai sayen kayan a kan farashi mai tsauri, bayan ga yadda darajar Naira ta fadi. Haka samun kudade na bukatun yau da kullum ya yi karanci, baya ga rashin fara biyan mafi karancin albashi da gwamanti ta yi aniyar yi, watanni da dama bayan hakan ya zama doka.

Duk dai irin abin da majalisar ta zartar a kan karin harajin, wanda shi ne mataki na karshe a kan lamarin, ya zama dole gare ta ta yi duba cikin tsanaki, kafin amincewa ko kin haka, bukatar gwamnati na son karin kudaden shiga kada ya sa a dora wa jama’ar kasa abin da ya fi karfinsu. Wannan karin kudin harajin a wannan lokaci bai dace ba, kuma abu ne da ya kamata a guje masa. Akwai hanyoyi kasuwanci da dama ga gwamnati kan yadda za ta habaka samun kudaden shigarta, barnatar da kudade a wasu hukumomi a fadin kasar nan da dakatar da yin haka kan iya bunkasa samun kudaden shiga maimakon karin kudin haraji a kan kayyayakin bukatun yau da kullum. Bayan haka kuma akwai karin hanyoyi da gwamnati ya kamata ta fadada na samun haraji a fannoni da dama, wadanda bincike ya nuna cewa wannan mataki shi ya fi jawo samun kudaden shiga maimakon kakaba wa mutane karin harajin kan kayayyakin bukatun yau da kullum da sauran harajoji.