✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada Buhari ya bai wa makiyansa mukamai – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi  kira ga Shugaban Kasa Muhammadu…

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi  kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, cewa kada ya kuskura ya bai wa makiyansa mukamai a gwamnatinsa.                                                                                                                                         Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne lokacin da yake gabatar da nasiha a Masallacin ’Yan-taya, da ke garin Jos a ranar juma’ar da ta gabata.

Ya ce bai kamata Shugaba Buhari ya bai wa mutanen da suka ki a sake zabensa karo na biyu mukamai ba.

Ya ce idan aka kuskura aka bai wa irin wadancan mutane mukamai a wannan gwamnati,  za su rusa  gwamnatin.

Har ila yau ya yi kira ga ’yan  Majalisar Dattawa da na Majlisar Wakilai da wakilan majalisun dokoki na jihohi su tsaya, wajen ganin an  nada mutane na kwarai a nade-naden da ake yi.

Ya ce, bai kamata wakilan majalisun su bari a nada mutanen da aka san barayi ba ne a wuraren da suka yi aiki a baya.

Ya ce “A yi kokari a zabo mana mutane  managarta a nade -naden da ake yi a gwamnatocin kasar nan, domin su taimaka wajen warware mana matsalolin da muke fuskanta a kasar nan.”

Ya yi kira ga malaman addinin Musulunci da na addinin Kirista da sarakuna da ’yan siyasa da sauran al’ummar kasar nan, su tashi tsaye wajen magance matsalar tu’ammali da miyagun kwayoyi da ake shigowa da su kasar nan.

Ya ce miyagun kwayoyin da ake shigowa da su kasar nan ne, suke jefa matasanmu cikin mummunan halin da suke ciki na aikata ta’addanci.

Daga nan ya yi kira ga maniyyata aikin Hajin bana da suke Kasa Mai tsarki su yi abin da zai kara daga darajar Najeriya, maimakon aikita laifuffukan da za su bata sunan kasarsu.