Da Dumi Dumi

Kada CBN ya ba da Dala don shigo da abinci – Buhari

Hamza Idris, Musa Abdullahi Krishi (Abuja) da Bashir Liman (Jos)

Shugaban  Muhammadu Buhari ya umarci Babban Bankin Najeriya da ya daina bai wa masu shigo da abinci  kudaden kasar waje a wani mataki na bunkasa harkar noma.

Ya ce kamata ya yi a adana kudaden da ke asusun kasar nan na kasashen ketare domin amfani da su wurin fadada tattalin arzikin “Maimakon ba da kudaden ga masu shigo da abinci daga kasashen waje.”

“Kada ku bayar da ko kwabo ga mutanen da ke son shigo da abinci cikin kasar nan,” kamar yadda mai magana da yawunsa ya ambato shi yana cewa lokacin ganawa da  gwamnonin APC a Daura ranar Talata da ta gabata.

Tattalin arzikin Najeriya shi ne mafi girma a Nahiyar Afirka amma duk da hakan ana shigo da abinci mai yawa daga kasashen ketare domin ciyar da jama’a.

Shugaba Buhari, wanda ya lashe zabe karo na biyu a farkon bana, ya yi alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Najeriya ce kasar da ta fi kowace hako danyen mai a Afirka kuma kudaden da ke fitowa daga fannin su ne kashin-bayan tattalin arzikinta.

Sai dai kaso mai tsoka na tafiya ne a tallafin shigo da abinci da sauran kayan bukatu na yau da kullum da kuma manyan injuna.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBC), ta ce a watanni uku na farko na bara, an kashe Dala miliyan 503 wajen shigowa da kayan abinci. Sai dai wannan adadin ya karu da kashi 25.84 a watanni uku na farkon bana.

Share