✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada ku bar mahandama su dawo gadon mulki – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi mutanen da suka cancanci kada kuri’a a Jihar Osun da kada su kuskura su bari a yi musu sakiyar…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi mutanen da suka cancanci kada kuri’a a Jihar Osun da kada su kuskura su bari a yi musu sakiyar da ba ruwa a zaben Gwamnan Jihar da za yi a gobe Asabar.

Ya ce “Kada ku zabi bara-gurbin dan siyasa a kan wannan kujera ta Gwamna wanda zai sa a koma gidan jiya tare da mayar da ku cikin duhu da Jihar Osun ta samu kanta a baya.”

Shugaba Buhari ya isa garin Osogbo ne a ranar Talata da ta gabata, domin nuna goyon baya ga dan takarar Gwamna da Jam’iyyar APC ta tsayar, Mista Gboyega Oyetola a zaben da za a yi a gobe Asabar. Da yake yi wa dandazon magoya bayan APC bayani a filin wasanni na Osogbo, ya ce, “Jihar Osun tana cikin jihohin da APC ke mulki a Najeriya da ya kamata ta ci gaba da kasancewa cikin wannan matsayi, musamman saboda irin ayyukan ci gaba da mulkin adalci da Gwamna Rauf Aregbesola ya shimfida cikin shekaru 8 da ya yi yana mulkin jihar.”

“Mun zo ne domin godiya ga Allah da Ya ba Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Rauf Aregbesola sa’ar kammala mulkin shekara 8 lami lafiya a jihar. Kuma mun zo ne domin rokon Allah Ya kare mu Ya ba mu ikon ci gaba da muhimman ayyuka a karkashin Gboyega Oyetola,” inji Shugaban kasar.

Ya kara da cewa, “Oyetola ya samu kyakkyawar shaida a tarihin rayuwarsa ta fannin kasancewa mai kishin kasa da gaskiya da rikon amana. Saboda haka muke yin kira ga duk wanda ya cancanci kada kuri’a ya zabe shi domin amfanin jihar da kasa baki daya.”

Shugaba Buhari ya yi wa al’ummar Jihar Osun alkawarin ganin Gwamnatin Tarayya ta kammala dukan muhimman ayyukan raya kasa da suka rataya a wuyanta, musamman manyan hanyoyin Iwo zuwa Ibadan zuwa Osogbo da Osogbo zuwa Ilobu zuwa Ogbomoso. Ya tabo wasu ayyukan raya kasa da ya ce nan ba da dadewa ba za a kammala su.

Shugaban ya yi ganawa ta musamman da sarakunan jihar a karkashin jagorancin Ooni na Ife Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi. An yi ganawar ce a gidan gwamnati da ke Osogbo kafin ayarin ya wuce zuwa filin wasanni na garin da aka gudanar da gangamin yakin zaben na gobe.

Manyan mutanen da suka rufa wa Shugaba Buhari baya zuwa gangamin na Osogbo sun hada da Sanata Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Jam’iyar APC ta kasa Kwamared Adams Oshiomhole da gwamnonin jihohin Kano da Legas da Oyo da Ogun da Ondo da Filato da Adamawa da Kaduna da Kebbi da Edo da Neja.

Wadansu daga cikin kusoshin Jam’iyyar APC da suka halarci taron sun hada da Cif Olusegun Osoba da Cif Bisi Akande.