Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kada ku sake zuwa da shanu yankinmu ta kasa – Gwamnonin Ibo

Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas sun gargadi Fulani makiyaya su daina kai shanu shiyyarsu a kasa ko ta cikin daji.

A sanarwar da Babban Daraktan Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas, Farfesa Simon Ortuanya ya fitar, ya ce wannan yarjejeniya ce da suka cimma da su makiyayan da ke zaune a yankin nasu. Ya ce kai shanu a kasa ta cikin daji ya zo karshe, sai dai sun amince su rika kaiwa cikin manyan motoci zuwa kasuwannin da ake sayar da su.

ADVERTISEMENT

Kungiyar ta ce “Daga yanzu ba za mu kyale wani makiyayi daga wata kasa ba ya shigo mana yankinmu da shanu ta daji, domin hakan ne ke jawo tashin hankali a tsakanin al’ummarmu da makiyayan.” Kungiyar ta kuma musanta jita-jitar da ake bazawa, cewa wai ta ba da fili a asirce ga makiyaya domin aiwatar da shirin RUGA.

“Gaskiyar lamarin shi ne, babu wani Gwamna daga wannan shiyya ta Kudu maso Gabas da ya ba da fili ko yake da niyyar bayarwa don aiwatar da shirin, domin mu ma ba mu da isassun filaye a wannan yanki,” inji kungiyar.

ADVERTISEMENT

Gwamnonin sun ce sun yaba da yadda suke da makiyaya masu bin doka, wadanda suke zaune a yankin tare. “Kai wadansu ma an haife su a nan kuma suna zaune lafiya da kowa. Har ’yan kwanakin nan da suka fara ganin wani sabon abu na mamaye filayemu da garkuwa da mutanenmu da kuma lalata gonakin al’umma. Wadannan makiyaya da muke tare da su, suna zaman lafiya da al’ummar wannan yanki. Sun ce wannan lamari da yake faruwa a gonakin jama’a, aikin makiyaya matafiya ne da suke kaura daga wata jiha zuwa nan jihohin Kudu maso Gabas, kuma akasarinsu ba ma al’ummar kasar nan ba ne,” inji Kungiyar Gwamnonin.

Ta kara da cewa ba za ta iya korar Fulanin da suke zaune lafiya tare ba, amma dai ba su da wani fili da za su bayar domin yin RUGA ko wurin kula da dabbobi.

Daga nan Gwamnonin suka yi kira ga mutanen yankin Kudu maso Gabas da ke zaune a wajen shiyyar, musamman wadanda suke shiyyar Arewa da kada su damu da wani faifan bidiyo da matasan Arewa ke yi musu barazana. Suka ce suna nan suna tautaunawa da Gwamnonin Arewa da shugabanni, kuma sun ba su tabbacin babu wani abu da zai samu al’ummarsu da suke harkokinsu a Arewacin kasar nan.

Sannan sun shawarci masu buga gangar yaki cewa su tuna da iyayensu da ’ya’yansu kuma su sake tunani, domin a lokacin yaki ko abokinka kan iya zama makiyinka. “Don haka kamata ya yi a zauna tare domin yadda za a gina kasa da ci gaban matasanmu, wadanda su ne manyan gobe, kaunar juna da sadaukar da kai da mance abin da ya faru a baya shi ne gimshikin gina kasa,” inji gwamnonin jihohin Ibon.