✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada mu yanke kaunar cin nasara a rayuwa (1)

Kamar yadda muka saba, yau ma Allah Ya sake kawo mu wani makon, kuma za mu ci gaba da kawo maku tambihi game da sinadaran…

Kamar yadda muka saba, yau ma Allah Ya sake kawo mu wani makon, kuma za mu ci gaba da kawo maku tambihi game da sinadaran yaukaka rayuwa. Jama’a, ina yi maku sallama, Assalamu alaikum.

Abu ne da kowa ya sani cewa rayuwarmu na cike da kalubale, wanda haka kan sanyaya gwiwar wasu, har ma su wofintar da dukkan al’amuransu, sannan su fitar da tsammanin samun nasara. Wannan bai dace ba, domin kuwa dama haka al’amuran rayuwa suka gada, idan yau an hau tudu, to gobe kuma sai a samu gangara, a gangaro zuwa ga nasara da cin ma bukata. Don haka, maudu’inmu na yau zai yi tsokaci ne game da wannan al’amari, yadda za mu fahimta da cewa bai kamata mu karaya da rayuwa ba, komai tsanani, komai runtsi.

Kamar yadda Allah Ya halicci mutum, ya sanya yanayin samuwarsa cikin mataki-mataki. Mutum kan faro ne daga digon maniyyi, ya koma tsoka, ya hadu da kashi, sannan a haife shi. Tun yana labubu, ya koma yana rarrafe, ya zo yana tafiya. Sannu a hankali har ya kai ga zuwa cikakken mutum, wanda zai iya tsinana wani abu a rayuwa. Ma’ana, ba lokaci daya ne halittar mutum kan tabbata ba.

To kuma haka rayuwar mutum ita ma take kasancewar, idan yana neman wani abu. Mutum zai fara neman abin ne daga mataki zuwa wani matakin. Idan ilimi yake nema, zai fara ne da zuwa makaranta, yau da kullum ana koya masa ilimin har ya kai ga ya samu nasarar zama masani.

Haka abin yake kasancewa ga manomi, ba rana guda ne zai tafi gona ya kama girbe dawa ko masara ba. Lallai ne sai ya bi al’amarin noman nan mataki-mataki. Sai ya yi jimirin hakurin daukar dukkan matakan da suka wajaba a gonar, sannan za ta kai shi ga matakin girbi da nasarar dibar amfaninsa. Manomin nan zai fara da share gona, ya yi huda, ya yi shuka, ya yi noma, ya yi huri, ya yi maimai; daga nan ya sake huda, sannan ya saurari ikon Allah.

A duk inda muka samu kanmu, kuma a duk yanayin da muka shiga, abu na farko da za mu sanya a zukatanmu shi ne, za mu iya yin nasara a rayuwa. Duk kalubalen da ya tare mana gaba, mu yi ta maza, mu tunkare shi gaba-gadi, sannan mu amince da cewa lallai za mu iya yin nasara a kansa. Ba zama za mu yi ba mu shantake, za mu sanya azama ne, sannan mu maida hankali yadda ya kamata, sannan mu bi hanya mafi dacewa da za ta kai mu ga biyan bukata. Idan muka yi haka, babu shakka ga nasara nan a hannunmu.

Sai dai wani abin da ya kamata ya zama fandeshi kuma ya zama abin da za mu rika tunawa da shi, shi ne, mu sanya a zuciyarmu cewa bayan wahala sai dadi. Don haka, a duk lokacin da muka fadi kasa a yayin cin ma wata bukata, kada mu dauka cewa wannan ne karshen rayuwarmu, kada mu dauka shi ke nan an yi ruwa an dauke, don haka ba za mu cin ma nasara ba. Kada mu yi haka, mu mike tsaye kawai, mu kakkabe jikinmu sannan mu sake tunkarar kalubalen; za mu ci nasara da yardar Allah.

Abin misali ga mutumin da ya tashi neman ilimi, kada ya ce zai same shi ne a cikin ruwan sanyi. Lallai ne sai ya nuna juriya da bin matakan da suka dace, sannnan zai samu irin ilimin da yake bukata. Aikinsa ne ya rika zuwa makaranta a kan lokaci ko kuma ya rika zuwa wajen malamin da zai dauki ilimin wurinsa a lokacin da suka kayyade.

Akwai ladubba da sharuddan da za a gindaya masa a makarantar ko kuma wadanda malamin zai gaya masa. Madamar yana son nasara, sai ya bi su yadda ya dace. Haka kuma, lallai ne ya mayar da hankali wajen bita da karatu da tambayar abin da bai gane ba, sannan ya samu abin da yake so.

Za mu ci gaba