Da Dumi Dumi

Kadan daga cikin tarihin Sarkin Zazzau

Aminiya ta tsakuro muku kadan daga cikin tarihin Mai martaba Sarkin Zazzazau Alhaji (Dr.) Shehu Idris na ɗaya wanda yana daya daga cikin manyan sarakunan Arewancin Najeriya. Wanda a makon da ya gabata ya cika shekara 45 bisa karagar mulkin kasar Zazzazau. Mai martaba sarki mutum ne masani, sannan kuma abin girmamawa a duk faɗin Arewa da sauran sassan Najeriya. Ɗaya daga ciki ɗimbin hikimomi da Allah ya yi masa ita ce tafiya da mutane a cikin mulkinsa, yakan tuntuɓi jama’a a kan abubuwan da ka-je-su-zo.

 

 

Haihuwarsa

An haifi Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dokta) Shehu Idris a 1937. Shi ɗan Malam Idris autan Sambo ne ɗan Sarkin Zazzau na 10. Malam Muhammadu Sambo kuma ɗan Sarkin Zazzau na 3 Malam Abdulkarimu Bakatsine.

ADVERTISEMENT

 

Karatunsa

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji  Shehu Idris, ya fara karatunsa na addini tun yana ɗan shekara biyar a hannun Malam Bawa da kuma Malam Abubakar da ke Unguwar Iya a garin Zariya.

A 1947, lokacin yana da shekara 11, Mai martaba Sarki ya fara karatun zamani a makarantar Elemantare ta Zariya (Zaria Elementary School), daga nan sai Makarantar Midil ta Zariya daga 1950 zuwa 1955. Bayan kammala wannan makaranta sai ya wuce zuwa Kwalejin Horar da Malamai ta Katsina (KTC) inda ya kammala a 1958.

 

Gogewa a aiki

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya fara karantarwa bayan kammala karatunsa a Katsina. Ya fara da koyarwa a makarantar firamare ta garin Hunƙuyi a 1958, daga nan kuma sai aka mayar da shi garin Zangon Aya, sannan sai Paki duk a matsayin Shugaban Makaranta (Hidimasta). Sannan an dawo da shi Zariya a matsayin Hedimastan Makarantar Firamare ta Ƙaura.

A 1960 ne ya zama Magatakardar Sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Muhammadu Aminu. Daga baya kuma ya zama Magatakardar Majalisar En’e ta Zariya a 1963. Sannan an naɗa shi Danmadamin Zazzau, Hakimin Birni da Kewaye a 1963, sarautar da ya riƙe har zuwa zamowarsa Sarki.

 

Zamowarsa Sarki

A 1975, bayan rasuwar Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu, sai masu zaɓen Sarkin Zazzau suka zaɓi Alhaji Shehu Idris a matsayin sabon Sarkin Zazzau, zaɓen da ya samu amincewa daga Gwamnatin Jihar Arewa ta Tsakiya wacce ke da hedikwata a Kaduna, a zamanin mulkin Gwamnan Soja Manjo Abba Kyari (wanda ya zama Birgediya Janar daga baya). Wannan naɗi nasa shi ya mai da shi Sarkin Zazzau na 18 a jerin Sarakunan Fulani, sannan Sarki na 3 a zuriyar Katsinawa.

 

Lambobin yabo da girmamawa

Saboda gudunmawar da ya daɗe yana bayarwa, musamman ta fuskar zaman lafiya da haɗin kai, Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya karɓi lambobin yabo da girmamawa da dama daga ciki da wajen Najeriya. Daga cikin irin waɗannan lambobi akwai Digirin Girmamawa na Dokta daga jami’o’i da dama da suka hada da: Jami’ar Kimiyya ta Tarayya da ke Minna da Jami’ar Najeriya da ke Nsukka da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da kuma Jami’ar Abuja.

Sannan a shekarar 2006, Ƙungiyar Tsofaffin Dalibai ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Alumni Association), ta karrama shi da lambar girmamawa kan gudunmawarsa  ga ci gaban kasa.

Mun ciro wannan tarihi na Mai martaba Sarkin Zazzau ne daga littafin: Dalhatu U. (2002). Malam Ja’afaru ɗan Isyaku, The Great Emir of Zazzau, wallafar Woodpecker Communication Limited. Zariya, Najeriya.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya