✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kafanin La Casera ya yi gangamin wayar wa matasa kai a kan illar shan kwaya

A makon nan ne Kamfanin lemon kwalba na La Casera ya fara gangamin wayar wa matasan kasar nan kai a kan illolin shan miyagun kwayoyi.…

A makon nan ne Kamfanin lemon kwalba na La Casera ya fara gangamin wayar wa matasan kasar nan kai a kan illolin shan miyagun kwayoyi. A cewar kamfanin, gangamin ya zama wajibi saboda yadda matasa ke tu’ammali da miyakun kwayoyi a kasar nan.

Da yake jawabi a kan dalilansu na shirya wannan gangami, Manajan Daraktan Kamfanin, Mista Chinedum Okereke ya ce matasa na da gagarumar gudunmawar da za su bayar wajen ci gaban tattalin arzikin kasar nan.

Ya ce hakki ne da ya rataya a kan kamfanin ya samo hanyoyin da za a yaki matsalar yadda matasa ke tu’ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan domin a ceto rayuwarsu.

Yanzu haka bincike ya nuna kashi 47 zuwa 50 cikin 100 na matasan kasar nan suna fama da matsalar shan kwaya wanda hakan ya sa kamfanin ya fara wayar wa mutane kai a kafafen watsa labarai a Jihar Kano da sauran bangarorin kasar nan.

“Wannan matsala ci gaba take yi a kasar nan don haka alhaki ne a wuyan kowa a  nemo hanyayoyin magance matsalar. Burinmu shi ne mu ilimantar da su a matsayinsu na matasa. Ta wannan gangami, muna fatar ilimantar da su  yadda za su kasance mutane nagari.

Wannan gangami za mu yi shi ne ta kafafen watsa labarai da suka hada da jaridu da gidan rediyo da talabijin da kuma kafafen sadarwa zamani na Intanet, ta haka ne za mu magance wannan matsala,” inji shi.

Mista Okereke ya ce wannan gangami zai taimaka matuka wajen wayar wa matasa kai domin su fahimci hadarin da yake tattare da tu’amali da kwayoyi.

“Kada ku yi tu’ammali da kwayoyi ko hada kwayoyi da abubuwan sha. Ku kauce wa matsi daga abokanku, ku zamo mutanen kirki. Tare za mu kawar da matsalar shan kwayoyi a tsakanin matasanmu,” inji shi.