Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kafin Gwamnatin Tarayya ta sayar da hannayen jarin Bankin Manoma

A ranar Alhamis 20 ga Disamban bara, Ma`aikatar Ayyukan Gona da Raya Karkara ta Tarayya ta yi shela a cikin wasu jaridun kasar nan, tana sanar da manya da kananan manoman kasar nan niyyar Gwamnatin Tarayya na sayar da kashi 40 cikin 100, na hannayen jarinta a Bankin Ayyukan Gona ga manoma. Sanarwar  mai sakin layi hudu da Babban Sakataren Ma’aikatar Dokta Abdulkadir Mu’azu, ya sanya wa hannu, wadansu daga cikin bayanan da ta kunsa sun kasance kamar haka: “Ana sanar da manoma da masu niyyar shiga aikin gona na kasar nan cewa Shugaban Kasa ya ba da umarni ga Hukumar Sayar da Kaddarorin Gwamnati ta sake fasalin Bankin Manoma. Tsarin da tuni ya yi nisa. Hakan zai karfafa wa manoma da masu sha’awar shiga ayyukan gona gwiwa wajen shiryawa su sayi hannun jarin Bankin Manoma a duk lokacin da aka gabatar da su. Kudirinmu shi ne Naira biliyan maitan da hamsin (Naira biliyan 250).

Sakin layi na uku da na hudu sun kara da bayanin cewa wannan dama ce gare ka  ka zama kana cikin wadanda ake sa ran su zama  masu jari a Bankin Manoma da zai rika ba ka damar samun lamuni mai sauki kuma mai karancin kudin ruwa. Domin karin bayani a tuntubi Dokta Abdulkadir Mu’azu, Babban Sakataren Ma’aikatar Gona da Raya Karkara, a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke yanki na 11, Garki Abuja

ADVERTISEMENT

Mai karatu, wadannan su ne bayanan abubuwan da sanarwar ta ce, duk kuwa da cewa shirye-shiye sun yi nisa, amma har yanzu babu wasu cikakkun bayanai da Ma’aikatar Gona da Raya Karkarar ta fitar a kan matsayin bankin game da darajar hannayen jarinsa, bare kiyasin kadarorinsa da yawan basussukan da ya ba da yau sama da shekara 40 da kafuwarsa da wadanda aka tabbatar za a samu biyansu da wadanda aka san an fitar da rai wajen biyansu, kai har da kiyasin darajar da kaddarorin da bankin yake da su a cikin kasar nan. Irin su gine-ginen ofisoshi da gidaje da kayayyakin aikin ofis, irin su kujeru da tebura da na’urori da makamantansu.

Hikimar samun haka ga mai son ya sayi hannun jarin wani banki ko kamfani ko masana’anta, bai wuce kada ya sayi abin da ba zai kawo masa riba ba, sai asara. Don haka ko shakka babu muddin mahukuntan Ma’aikatar Ayyukan Gona da Raya Karkara ta Tarayya da na Hukumar Sayar da Kadarorin Gwamnati suna son manoma da masu sha’awar shiga ayyukan gona na kasar nan su amsa wancan kira, to ya zama wajibi, tun tafiya ba ta yi nisa ba yadda ta ba da waccan talla za a sayar,  ta sake fitar da kwankwacinta da za ta yi wa ’yan kasa dalla-dallar matsayin da bankin yake ciki.

ADVERTISEMENT

Ko shakka babu Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da take neman shekara hudu a karagar mulki, ta rungumi ta tallafa wa manoman kasar nan sosai, musamman manoman shinkafa da masara da dawa da sauransu, bisa niyyarta ta hana shigo da kayan abinci daga kasashen waje, musamman shinkafa. Bayan da ta kaddamar da shirin a karon farko a Jihar Kebbi a karshen shekarar 2015. A karshin wannan shiri zuwa yanzu gwamnatin ta kashe biliyoyin Naira bisa ga irin yadda ta fadada shirin cikin kasa, ta yadda kowa zai ji ana yi da shi, da kuma kokarin da take yi na ganin abinci ya wadata a kasar nan, mun daina shigo da shi daga kasashen waje, musamman shinkafa.

Sai dai kuma kash! Babban abin takaicin da ake fama da shi, bai wuce irin yadda tunda aka fara shirin bisa ganganci ko  rashin sanin kimar kai ce ta sanya akasarin manoman da suka ci gajiyar shirin ba sa son su biyan bashin, duk da cewa sun ci riba. Hakan ya sanya ana ta muhawara a tsakanin  manoman cewa ba manoman gaskiya aka ba tallafin ba a fadarsu, manema ko masu uwa a gindin murhu aka ba, shi ya sa biyan ya gagara. Alhali a Jihar Kaduna a ’yan kwanakin nan ina ta jin sanarwar Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa reshen Jihar tana ta kiraye-kiraye ga ’ya’yanta kan lalle su hanzarta biyan kudaden rancen da aka ba su, kafin ta fara gurfanar da masu kunnen kashi a gaban kuliya.

Mai karatu abin da ya sa na kawo maka wannan batu na irin yadda Gwamnatin Tarayya ta rungumi ayyukan gona gadan-gadan da yadda wadanda suka amfana da tallafin suke nokewa wajen kin biyan bashin da aka ba su, bai wuce in kawo ka gabar yadda wadansu  masana harkokin tafiyar da bankuna suke da fargabar cewa, bayan wadancan matsaloli da na ambata a sama na rashin sanin matsayin da Bankin Manoman ke ciki, akwai kuma fargaba kan wadanda za su mallaki hannayen jarin bankin, bisa la’akari da cewa, yau sama da shekara 20, ke nan da gwamnatin tsohon Shugaban Kasa marigayi Janar Sani Abacha ta rika yi wa ’yan hukumomin daraktoci da na gudarwar wasu bankun kasuwancin kasar nan dirar mikiya da aka samu da laifin sun daka wawa a kan kudaden masu ajiya a bankunansu, al’amarin da ya kai har kotuna suka rika daurewa da kwace dukiyoyin irin wadancan mayaudara da aka samu da laifi, amma ka ce har yanzu ba a tsabtace fannin ba. Don kuwa ko a ’yan watannin nan, sai da Gwamnatin Tarayya ta kori biyu daga cikin ’yan Hukumar Daraktoci da Manajin Daraktan Bankin Daimond, bisa zargin sun wawure kudaden masu ajiya a bankin.

Irin wannan makoma masana harkokin bankin suke gudun ta faru da kudaden manoman da suka sayi hannayen jarin Bankin Manoman. Wadansu kuma suna fargabar cewa gwamnati ta ci gaba da rike kashi 60 cikin 100, na hannayen jarin bankin ana nan dai kamar yadda ake yanzu da Gwamnatin Tarayyar ita ke da wuka da nama wajen nada shugaba da mafi yawan wakilan Hukumar Daraktoci da shi kansa Manajan Daraktan, da za su ci gaba da yin abin da suke so da kudade da kadarorin bankin.

Mafita kawai a ra’ayin masana harkokin banki, ita ce tunda wannan gwamnati tana matukar son inganta ayyukan noma da kiwo, to, kamata ya yi ta shige gaba manoman da kansu su kafa bankunansu, kamar yadda kasashen Noway da Siwidin da Denmak suka dade da yi. Allah Ya ba da sa’a.

Ina son in yi amfani da wannan dama wajen mika ta’aziyyar wannan fili ga iyalai da ’yan uwa da aminai da Shugaban Kasa da Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Jihar Sakkwato da mutanen jihar da daukacin jama’ar kasar nan bisa ga babban rashin da aka yi na tsohon Shugaban Kasa na farar hula a Jamhuriya ta Biyu, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari da Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Juma’ar da ta gabata a Asibitin Kasa da ke Abuja, bayan gajeriyar jinya, yana da shekara 93, a duniya. Wannan fili yana rokon Allah SWT Ya jikansa Ya sa ya huta, tare da ba iyalai da ’yan uwansa da daukacin ’yan Najeriya baki daya hakurin jure rashin  tare da kyautata tamu zuwan amin summa amin.