✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kafofin sada zumunta na zamani babban hadari ne ga Najeriya – Farfesa Tukur

Wani tsohon dan jarida kuma malami a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Hussaini Tukur ya ce kafofin sada zumunta na Intanet, babban hadari…

Wani tsohon dan jarida kuma malami a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Hussaini Tukur ya ce kafofin sada zumunta na Intanet, babban hadari ne ga Najeriya.

Farfesa Hussaini Tukur ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da aka shirya wa ’yan jarida kan yadda ya kamata su rika daukar labarai a garin Jos.

Ya ce wadannan kafofin sada zumunta suna da muhimmanci a harkokin rayuwa, amma kuma suna da illa matuka. Domin mutum zai iya daukar wayarsa, nan take ya yi rubutun batanci ko kuma na wani abu ya aika, cikin mintuna kalilan miliyoyin mutane su gani.

Farfesa Tukur ya ce a Najeriya ba a amfani da kafofin sada zumunta ta hanyar da ta kamata. “Domin a Najeriya yanzu za ka ga an dauki wani rikici ko wani hadarin mota, ko wani mugun abu a yada wa duniya. Irin wadannan abubuwa suna kawo sabani a tsakanin al’umma inda suke sanadin jawo rikice-rikicen da ake rasa rayukan jama’a,” inji shi.

Farfesa Tukur ya ce a yanzu duk labarin da ka gani a kafofin sada zumunta, sai mutum ya yi tambayoyi da dama kan sahihancinsa, ya ce don haka wadannan kafofin sada zumunta suna jefa mutane a cikin rudani.

Ya kara da cewa a kasashe da dama sun a amfani da kafofin sada zumunta, don ci gaban kasa. “Amma mu a Najeriya ba ma amfani da su wajen ci gaban kasa,” inji shi.