✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kai shugabannin kananan hukumomin Zamfara Dubai almubazzaranci ne’

daya daga cikin ’yan jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Zamfara Alhaji Abdulhadi Sa’idu ya ce almubazzaranci ne da Gwamnan Jihar Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar…

daya daga cikin ’yan jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Zamfara Alhaji Abdulhadi Sa’idu ya ce almubazzaranci ne da Gwamnan Jihar Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ya kwashi shugabannin kananan hukumomin jihar zuwa Dubai ko ma da wace iri manufa ce.
Alhaji Abdulhadi ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gusau, inda ya ce tattaunawar da Gwamnan zai yi da shugabannin kananan hukumomin ana iya yin sa a ko’ina koda a ofishin kantoma ne, ba sai ya kwashe su zuwa wata kasa ba, saboda sirri. Ya ce to ai ba sirri ba ne don jama’a suna da labarin abin da za su tattauna a kai, ba sai an kwashei dukiyar al’umma an yi almubazaranci ba.
Ya ce idan aka dubi abin da aka ce ya kai su Dubai, kamar kara masu lokaci da kara musu kudi da sauransu, ya nuna cewa gwamnati ta nuna wa al’umma cewa shugabannin kananan hukumomi ba zabensu aka yi ba nada su aka yi, kuma kara musu wa’adin mulki ya haramta gare su .
Ya ce su a Jam’iyyar PDP, wadanda Gwamnan ya fita da su dama ba su dauke su zababbu ba, kantomomi suka dauke su, don haka Gwamnan yana da dama ya dauke su ya kara nada su kamar yadda ya nada su a wancan lokaci.
Da yake tsokaci kan ayyukan da Gwamnan ke yi a kananan hukumomin, Alhaji Abdulhadi ya ce idan aka dubi aikin da ake yi a cikin garin Birnin Magaji, kafin a shiga garin daga kauran Namoda kowa ya san irin wahalar da ake sha, musamman da damina, duk dan garin Birnin Magaji ya fi so a karasa masa hanyar nan, maimakon aikin cikin gari.