✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara farashin man fetur zuwa N151.56 a Najeriya

An kara farashin litar man fetur zuwa Naira 151.56 inji hukumar PPMC mai kayyade farashin mai

Gwamnatin Tarayya ta kara farashin man fetur zuwa Naira 151.56 duk lita kamar yadda Hukumar kayyade farashin man fetur a kasar PPMC ta sanar.

Hakan na kunshe cikin sanarwar da shugaban hukumar shiyyar Ibadan, D.O Abalaka ya fitar a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2020.

Yana cewa: “Ku sani cewa mun sanya sabon farashin sayar da man fetur kuma a yanzu farashin sa zai koma naira dari da hamshin da daya, da kwabo hamsin da shida duk lita.”

“Wannan sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 2 ga Satumban 2020,”inji shi.