Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kakaba wa Ayatollah Khamenei takunkumi zancan banza ne – Shugaban Iran

Shugaban Iran

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya mayar da martani dangane da takunkumin da Amurka ta sanya wa Jagoran addinin Iran din, Ayatollah Khamenei.

Rouhani ya kara bayyana takunkumin da aka sanya wa Ayatollah Khamnei da kuma wanda aka yi barazanar kakaba wa Ministan Kasashen waje na Iran da “zancen banza”.

ADVERTISEMENT

Har wa yau, Shugaban na Iran ya kuma bayyana Fadar White House a matsayin ‘sokwaye’.

Shugaba Donald Trump ne dai ya ce zai kakaba wa kasar Iran takunkumi mai tsauri wanda zai shafi shugaban addini Ayatollah Khamenei kai-tsaye.

ADVERTISEMENT

Mista Trump ya ce ya dauki matakin ne bisa harbo jirgin saman kasar mara matuki da Iran din ta yi da kuma “laifuka da yawa”.

“An kebance Ayatollah Khamenei ne saboda shi ne ke da alhakin duk abin da gwamnatin Iran take aikata wa,” in ji Trump.

Rashin jituwa dai na kara tabarbarewa a tsakanin kasashen biyu a ’yan kwanakin nan.

Sakataren Baitil Malin Amurka Stebe Mnuchin ya ce wannan takunkumin zai shifi biliyoyin Daloli na kadarorin Iran, wanda dama can ya fara aiki tun kafin ta harbo jirgin na Amurka a yankin Gulf a makon da ya gabata, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ministan harkokin wajen Iran Jabad Zarif ya ce shugaban Trump “ba ya la’akari da tsarin diflomasiyya kuma burinsa kawai shi ne a tafka yaki.”

Za mu ci gaba da harbo jiragen Amurka – Iran

Da yake kara jawabi a game da takun sakan, Kwamandan Rundunar Sojin Ruwan Iran Huseyin Hanzadi ya mayar wa da Amurka martani game da sukar su da ta yi bisa harbo jirgin yakinta mara matuki inda ya ce idan wani jirgin saman Amurka ya sake karya ka’idar sararin samaniyarsu za su harbo shi nan da nan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Fars ya ruwaito Hanzadi na fadin cewar “Abokiyar gaba Amurka ta aike da jirgin saman ta mara matuki na leken asiri zuwa yankin da ta da hurumi kuma ta ga an harbo shi. Muna bayyana wa karara idan haka ta sake faru wa to mu ma za mu harbo jirgin saman. Duk wani makiyi ya san hakan.”

A ranar Alhamis din makon jiya ne Dakarun Ruwa na Juyin Juya Hali na Iran suka harbo jirgin sama Amurka mara matuki samfurin RK-4 Global Hawk a gabar tekun Oman bayan ya shiga iyakar kasarsu ba bisa ka’ida ba.

Cibiyar Tsaro ta Amurka kuma ta fadi cewar jirgin bai shiga iyakar Iran ba, yana tafiya ne a sararin samaniyar kasa da kasa.

Sakamakon haka ya sanya Trump kiran taron gaggawa domin mayar da harin martani ga dakarun Iran amma sakamakon yadda ya fahimci mutane da yawa za su iya rasa rayukansu ya sanya shi fasa wa.

Yaki da Iran zai yi muni matuka- Shugaba Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce baya neman yaki da kasar Iran kuma yana niyar tattaunawa da shugabanninta ba tare da wasu sharuda ba, amma kuma ya ce ba za a kyaleta ta ci gaba kera makaman kare dangi ba.

Trump ya fada wa taron manema labaran NBC cewa idan Amurka ta shiga yaki da Iran za a ga abin da ba a taba gani ba, saboda lamarin zai yi muni matuka, kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Shugaban na Amurka ya ce, “ba za ku iya mallakan makaman nukiliya ba. Idan kuma kuna so mu tattauna kofa na bude. In kuwa ba haka ba za ku ci gaba da fuskantar takunkuman tattalin arziki lokaci mai tsawo.”

Manyan jami’an Amurka a kan tsaro da suka hada da mai bada shawara a kan tsaro John Bolton da Mataimakin Shugaban Kasa Mike Pence sun yi wa Iran kashedi cewa kada ta dauki janye wa da Trump ya yi na mayar da martanin a kan harbe jiragen Amurka mara matuka a yankin tekun Hormuz a matsayin rauni daga Amurka.