✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kakar Wasa: Neymar ya kauracewa motsa jiki na Kulob din PSG

Kungiyar Kwallaon Kafa ta Paris Saint Germain, ta tabbatar da cewa, dan wasanta Neymar Junior, ya ki komawa babban birnin Faransa, dan halartar horaswar kungiyar…

Kungiyar Kwallaon Kafa ta Paris Saint Germain, ta tabbatar da cewa, dan wasanta Neymar Junior, ya ki komawa babban birnin Faransa, dan halartar horaswar kungiyar gabanin fara kakar wasanni ta bana—hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta yamadidin yi wuwar barinsa kulob din na PSG.

An yi ta rade-radin cewa, Neymar din ya zaku matuka na ya koma taka leda a tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona.

Tun da farko dai, wata Jaridar Wasanni a Sifaniya ta ruwaito cewa, dan kasar Brazil din hankalinsa ya riga ya bar PSGn ya koma Barcelona, kuma bai da niyyar ya sake sanya kafarsa a filin atisayen PSGn.

A cewar rahoton Jaridar, Neymar din ya kuma nemi Barcelonan da ta gaggauta sanya hannu kan komewarsa kungiyar.