Da Dumi Dumi

Kalaman Osinbajo kan zaben 2023 sun tada kura

Osinbajo and Faruk

A makon jiya ne Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo,  yayin neman goyon baya a Kudu maso Yamma ya bayyana cewa ya kamata al’ummar yankin su sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari a zabe badi, domin su samu damar darewa mulki a shekarar 2023.

Farfesa Osinbajo ya ba al’ummar yankin Kudu maso Yamma tabbacin cewa Buhari zai mika musu mulki idan ya kammala zangonsa na biyu, al’amarin da ya tada kura kuma ya jawo hankalin sauran sassan Najeriya da ke da bukatar hawa kujerar a shekarar 2023.

Babban Daraktan Rediyon Muryar Najeriya Mista Osita Okechukwu shi ne wanda ya fito daga yankin Kudu maso Gabs ya bayyana ikirarin na Mataimakin Shugaban Kasa da wata ankararwa ce ga al’ummar Ibo ka su mike tsaye su zabi Buhari a zaben mai zuwa domin su samu karbar mulkin a shekarar 2023.

A yayin da yake jawabi ga ’yan jarida a Enugu a farkon wannan mako, Mista Osita ya ce: “Kuri’unmu ga Buhari za su karfafa na dimbin magoya bayansa da ke Arewa, domin kuwa yana da dimbin magoya baya daga miliyan 10 zuwa 12, don haka wannan babban adadi ne. Goyon bayanmu ga Buhari ya doru ne kan yadda yake samar da manyan ayyyukan raya kasa, musamman aikin Gadar Neja ta Biyu, aikin hanyoyi da suka kai tsawon kilomita 5,000 da titin jirgin kasa mai tsawon kilomita 5,000 da samar da karin wutar lantarki ta megawatt 5,000 da kuma kokarin bunkasa noma domin dogaro da kai.”

Shi ma Gwamnan Jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha ya ce babu wanda ya isa ya hana shi yin takara a zaben na 2023. Yayin da Jam’iyyar PDP ta bayyana kalaman na Osinbajo da kokarin karkatar da al’ummar Yarabawa daga rashin alkiblar gwamnati mai ci.

ADVERTISEMENT

A martanin da Alhaji Faruk Adamu Aliyu tsohon Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai kuma daya daga cikin makusantan Shugaba Buhari ga Jam’iyyar PDP, kan sukarta ga kalaman na Osinbajo, Faruk Aliyu, ya ce bayanin Farfesa Yemi salon yakin neman zabe ne kawai ba zaunanniyar matsaya ta jam’iyyarsu ba.

“Misali mutum biyu ne ke neman amarya, wannan ga salonsa na neman nasara, shi ma wancan ga nasa salon, to ina ruwan daya da salon daya? Kowa na matsayin abokin hamayya, illa kawai dalilai da kuma tasirorinsa ya fisshe shi. Wannan shi ne abin da ke faruwa a siyasance,” inji Faruk Aliyu.

Ya ci gaba da cewa, “Idan Mataimakin Shugaban Kasa a matsayinsa na mutum dan Adam ya yi sha’awar ya karbi ragama ta Shugabancin Kasa sannan ya bayyana abin da yake so ga al’ummarsa, ai ina ganin yana da dama ya fadi haka a matsayinsa na dan Najeriya. Babu wanda ya isa ya hana shi bayyanawa. Sai dai wannan ba ya nufin matsaya ce ta jam’iyya a siyasance ba.”

Jigon a Jam’iyyar APC ya yi watsi da zargin kuntata wa al’ummar Arewa mazauna yankunan kan iyaka da ketare, ta hanyar hana al’ummarsu ayyukan fito, musamman abin da ya shafi shinkafar waje, inda ya ce wannan gata ce Gwamnatin Buhari ta yi musu don ta maida su masu dogaro da kai a fuskar noma, maimakon kasancewa dillalai ga manoman kasashen waje.

Ya ce tsarin wanda ya magance amfani da kudin kasar nan a fuskar shigo da shinkafar waje, zai kuma taimaka wa tattalin arzikin kasar nan maimakon dogaro da bangaren man fetur kadai. “Haka ba gaskiya ba ce a ce ayyukan da gwamnatin nan ke yi ta fi fifita yankin Kudu fiye da Arewa, illa dai wasu ayyukan gwamnatin ta gaje su ne daga wajen wacce ta gabace ta, amma ta gaza yin su kuma ba daidai ba ne a yi watsi da su a yanzu saboda kawai Buhari ba dan yankin ba ne. Wannan ya nuna adalci irin nasa,” inji shi.

Ya ce akwai ayyuka masu yawa da gwamnatin ke aiwatarwa a yankin Arewa ta fuskar wutar lantarki da tituna da layin dogo da kuma bututun gas. Haka nan ya ce wadansu da ke Kudu kamar na Legas zuwa Ibadan aiki ne da ya shafi kasa baki daya da ya ce Jam’iyyar PDP ta gaza yi a tsawon mulkinta na shekara 16.

Game da matsalar tabarbarewar harkar tsaro a wasu yankunan kasar nan musamman a Jihar Zamfara da wasu hanyoyi a Jihar Kaduna, dan siyasar ya ce wannan wani sabon salo ne na matsalar tsaro da ya ce gwamnatin za ta yi dukan mai yiwuwa a yanzu don ganin karshensa. Sai dai ya ce bai kamata ’yan Najeriya su mance da matsalar bama-bamai ba da ya ce gwamnatin ta Buhari ta samu nasarar sosai a kai.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya