✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kalubale: Shin kan marubuta zai hadu kuwa?

An gabatar da wannan jawabi ne a dakin taron murnar cika shekara daya da kafuwar ‘Duniyar Marubuta,’ zauren marubuta na internet, wanda aka gudanar a…

An gabatar da wannan jawabi ne a dakin taron murnar cika shekara daya da kafuwar ‘Duniyar Marubuta,’ zauren marubuta na internet, wanda aka gudanar a Lahadin da ta gabata, a garin Kankiya, Jihar Katsina:

Daga Ado Ahmad Gidan Dabino

Gabatarwa: Marubuta mutane ne na daban, ba wai sun fi sauran rukunonin bil’adama ba ne, a’a, sai dai su daban suke da sauran mutane; wato ’yan baiwa ne, sannan shi kansa rubutun baiwa ne. Marubuta na yin tunani ne iri na daban, suna kuma kallon rayuwa da al’amuran rayuwa da wata irin fahimta tasu ta daban, sannan su bayyana ta a rubuce, wato su kawo nesa kusa, su kuma kawo bara bana.
“Marubutan adabi mahaukata ne.” Inji Donne Chikere, ANA Katsina, 2011. Mahaukata ba masu duka ba, mahaukata ba masu zantuka na rashin hankali ba, mahaukata ba masu rasa tunani ba, a’a, yana nufin mahaukata masu jin kansu da nuna isa, wadanda suke cin kansu da kansu, masu zama su yi ta gardama da sukar juna, wani lokacin babu gaira babu dalili, sai don kawai neman suna da son iyawa ko tozarta juna. Za a iya tabbatar da wannan hasashe, idan aka yi duba na tsanaki da yadda marubuta suke daukar kansu sun fi kowa hankali da tunani ko saita rayuwar jama’a.
Chikere, ya kara da cewa: “Ka taba ganin taron mahaukata sun tsinana abin kirki?” Ya koka wa Khalid Imam ne ta hanyar nuna damuwarsa game da yadda gungun marubutan Nijeriya suka hadu a taron ANA Abuja 2011, lokacin da ake ta takaddama a kan zaben da za a yi a waccan shekara, tsakanin Jeri Agada da Remi Raji, amma kasuwar bukata da son zuciya sun jawo ana ta ci wa juna mutunci da batanci da bi-ta-da-kulli da cin dunduniya a idon ’yan jaridun duniya, ba tare da kunya ko lura da mutuncin juna ba, kawai don neman kujerar shugabanci.
A ranar Juma’a 25-31 ga watan Agustan 2008, a wani rubutu da aka buga a cikin jaridar Leadership Hausa mai taken ‘Marubuta a kan sikeli’, wanda Malam Buhari Daure, Daura Katsina ya yi, ya kira marubutan Hausa da marasa ilmi, ‘mahaukata, ’yan banza kuma ’yan iska’ kamar yadda ya rubuta a takardarsa, a sakin layi na bakwai, layi na karshe.
Shi kuma Sam Nda-Isaiah, mawallafin jaridar Leadership, a jawabinsa a wajen taron marubuta na Arewacin Najeriya da aka yi a Jihar Kebbi, ranar 17/6/2013, ya bayyana cewa: “In kana so ka mutu a cikin talauci, to ka zama marubuci a Nijeriya.”
Babu shakka, duk wanda ya yarda kuma yake jin cewa ya fi kowa a wannan rayuwa, to, labudda ya fi zama mahaukaci a kan wanda bai dauki wannan ra’ayi ba.
Da yawa marubuta ba sa son gyara ko daukar shawara da za ta bunkasa rubutunsu, yin gyara sai ya zama fitina da tashin hankali a tsakaninsu kuma da yawa wasu marubuta suna kawo gyara don son iyawa da tozartawa, ba don akwai sahihin gyara ba. Kuma duk duniya an yarda rubutu ba aikin mutum daya ba ne, sai an duba an gyara an ba da shawarwari don a samar da inganci, ba daga-buhu-sai-tukunya ba (sunan wata shinkafa), kuma wannan daga-buhu-sai-tukunya, shi ne babban rashin adalci da ake yi wa rubutu, wanda hakan na jawo rashin hadin kai tsakanin wasu marubuta da makaranta da masana a jami’o’i, har ma suke raina harkar; suke yi mata rikon sakainar kashi.
Masu jin haka a ransu, ana sa ran za su iya hada kai salun alun kuwa? Sai dai in sun ga uwar bari, wata musifa ko bala’i ya tunkaro su, suka ga ba makawa zai cinye su, to sannan wata kila za su nemi zama inuwa daya (misali, rigimar Hukumar Tace Fina-finai da dab’i ta Jihar Kano, 2010); shi ma na dan wani lokaci kafin ungulu ta koma gidanta na tsamiya.
Kuma zai yi wuya a kowace jiha ta Najeriya da za ka je ba ka samu matsalolin rashin hadin kai a tsakanin marubuta ba, wanda shi ne makasudin zaman doya da manja. Kamar yadda Muhammad Suleman Gama, Kano, cikin shirinsa na rediyo yake cewa, siyasa kasuwa ce; duk wanda ka gani a kasuwar bukata ce ta kawo shi.
Akwai wasu abubuwa da suke haifar da rashin hadin kai a tsakanin kungiyoyin marubuta da kuma su kansu marubutan.
Wasu daga cikin abubuwan da suke haifar da rashin hadin kai:
1-Rashin yarda da juna. 2-Rashin girmama da kuma raina na gaba. 3-kin yi wa juna uziri. 4-kokarin tozarta juna. 5-Rashin kunya. 6-Son zuciya. 7-Ganin ba wanda ya isa. 8-Ganin ba wanda ya iya sai ni. 9-Gaba. 10-kyashi. 11-Mayar da kungiya kayan gadon gidanmu. 12-Bakin ciki. 13-Hassada. 14-Cin mutuncin juna. 15-Gulma da tsegumi. 16-kokarin tade wani.
Wasu daga cikin abubuwan da za su kawo hadin kai:
1-Girmama na gaba. 2-Hakuri da juna. 3-Yafiya. 4-Yi wa juna uziri. 5-Guje wa son zuciya. 6-Sanya ci gaban rubutu a gaba ba bukatun son zuciya ba. 7-Daina jin na fi kowa ko ni kadai na iya. 8-Taimaka wa juna. 9-Yarda da gyara da ba da shawararwari don inganta rubutu cikin kyakkyawar niyya. 10-Mu gudu tare mu tsira tare. 11-Zama a yi tsari na gaske don ci gaban marubuta. 12-Gaskiya da amana. 13-Kawar da bambanci da fifita wasu a tsakanin ’ya’yan kungiya. 14-Rige kwadayin mulki na ko a mutu ko a yi rai. 15-Rage gulma da tsegumi. 16-Daina yarda da zuga.
Za mu kammala