✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kalubalen da Gwamna Babagana Umara ya fuskanta a kwana 100

Duk da cewar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara, ya gaji wasu ayyuka da gwamnatin baya ta faro ba ta kammala ba, musanmman gine-ginen makarantu da…

Duk da cewar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara, ya gaji wasu ayyuka da gwamnatin baya ta faro ba ta kammala ba, musanmman gine-ginen makarantu da ma’aikatu da asibitoci a garin Maiduguri da wasu daga kananan hukumomi da yakin Boko Haram ya daidaita, a kwana 100 gwamnatinsa ta ci gaba da fuskantar kalubalen da suka hada da mayar da ’yan gudun hijira  garuruwansu da kuma hare-haren Boko Haram.

Wakilinmu ya ce Gwamna Babagana Umara ya shaida wa manema labarai cewa ya mayar da hankali ne kacokan a kan gyaruwar al’amura da harkar tsaro ta yadda za a ji dadin  gudanar da ayyukan ci gaba ga al’umman jihar.

Ya kuma ce Gwamna Babagana ya kori wadansu ma’aikata da manyan jami’an gwamnatin jihar da na wasu kananan hukumomi kan zargin sakaci da aiki, sa’annan ya bayar da umarnin farfado da cibiyoyin samar da ruwan sha ta yadda jama’a za su sami tsabtataccen ruwa a wuraren da suka kamata.

Gwamna Umara ya kuma ziyarci wasu daga cikin  kananan hukumomin da yakin Boko Haram ya daidaita su inda ya duba barnar da suka yi ya kuma bayar da tabbacin kare rayuka da dukiyoyin alummar yankunan da abin ya shafa, kuma ya karfafa wa kungiyoyin sa-kai na Sibiliyan JTF da ’yan banga da maharba ta ba su duk goyon bayan da ya kamata don kawo karshen ayyukan ta’addancin Boko Haram a jihar.

Gwamna ya rantsar da sababbin kwamishinoninsa ne ana sauran kwana 15, ya cika kwana100 a karagar mulkin jihar, bayan  Majalisar Dokokin Jihar ta kammala tantance sunayen da ya mika mata don nadawa a matsayin kwamishinoni. Lokacin rantuswar  ya hori sababbin kwamishinonin su kamanta gaskiya da rikon amana da kuma yin aiki tukuru don ciyar da jihar gaba. Kuma ya kara da cewa kada wani kwamishina ya shigo gidan gwamnati in ba tare da an gayyace shi ba.