kalubalen tsaro da Najeriya ke fusknta ya hana Obama zuwa kasar – Ben Rhode

Obama ya fara ziyarar kwana takwas a nahiyar Afirka, inda zai ziyarci kasashen Senegal da Afirka ta Kudu da Tanzaniya, amma ban da Najeriya, al’amarin da Mataimakin Mai bai wa Shugaban kasar Amurka Shawara kan Harkokin Tsaro, Ben Rhode, wanda ya yi wa ’yan jarida bayani, ya bayyana cewa Najeriya na fama da matsalar tsaro, kuma Amurka ta hada kai da kasar don shawo kan wannan babban kalubale.
Shi ma Darakta mai kula da Harkokin Afirka, Geant Harris da Babban Mai Bunkasa Harkokin Dimokuradiyya, Gayule Smith, sun ce Najeriya na fama da babban kalubalen tsaro a halin yanzu. Don haka za ta yi hadin gwiwa mai karfi da Amurka, wajen shawo kan matsalar. Muna da tabbacin cewa, mun samu damar hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya. A dai irin wannan yanayi ba za mu iya ziyartar Najeriya ba.”
Tsarin da aka shirya na ziyarar Shugaba Obama a Afirka, an kebance Afirka ta Kudu da Afirka ta Yamma da Gabashin Afirka. Ita kuwa Senegal an zabeta ne saboda ita ce kasar da Musulmi ked a dimbin yawa, kyuma ita rainon Faransa ce, don haka take da matukar muhimmanci ga Amurka, musamman kasancewar dimokuradiyya ta kafu a kasar.
Sai dai Mista Rhode ya ce Najweriya na da matukar muhimmanci wajen samar da kyakkyawar makoma ga Afirka, kuma Amurka na da dimbin jari a kasar, tare da hadin gwiwarta wajen jagorancin kasashen da ke cikin kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin afirka ta Yamma (ECOWAS). Ya ce wannan ziyara dam ace ga Shugaba Obama wajen fadada harkokin Afirka, a farkon zangon wa’adin mulkinsa na biyu. “A hakikanin gaskioya muna ganin Afirka a matsayin nahiyar da ke da matukar muhimmanci a duniya, kuma wurin da Amurka ke kokarin samun kafuwa nan da shekaru masu zuwa. Akwai yanayin bunkasa tattalin arziki a yankin, ta hanyar bunkasa ciniki da kara saka hannun jari ga harkokin kasuwancin Amurka, acewarsa.

Share