✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kama mafarauta 13: Shugabannin Arewa su hana zuwa farauta a Kudu–Fadar Hausawa

Fadar Sarkin Hausawan Ado-Ekiti a Jihar Ekiti ta yi kira ga gwamnatocin Arewa su hanzarta hana mutanensu zuwa yawon farauta a Kudu saboda yadda mutanen…

Fadar Sarkin Hausawan Ado-Ekiti a Jihar Ekiti ta yi kira ga gwamnatocin Arewa su hanzarta hana mutanensu zuwa yawon farauta a Kudu saboda yadda mutanen yankin suke kallonsu a matsayin ’yan Boko Haram ko masu satar mutane. Kiran ya fito ne daga bakin mai jiran gadon Sarautar Hausawan Ado-Ekiti Alhaji Abdullahi Yusuf, bayan kama wadansu mafarauta 13 ’yan asalin Jihar Kano da Rundunar ’Yan sandan Jihar Ekiti tayi a ranar Juma’a da ta gabata.

Alhaji Abdullahi Yusuf ya ce, “Bai dace a rika ganin mutane dauke da kananan makamai suna tasowa daga Arewa domin yawon farauta a dazukan Kudu a irin wannan lokaci na tabarbarewar tsaron ba.

Dole ne mutanen da ke zaune a kauyukan da mutanen suke zuwa yawon farauta su zarge su da wata manufa daban. Saboda haka muke kira ga gwamnatocin jihohin Kano da Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Katsina da Jigawa da Neja su hanzarta daukar tsauraran matakan dakatar da irin wadannan mutane tasowa daga garuruwansu na asali zuwa Kudu da sunan farauta domin guje wa tayar da zaune-tsaye.”

Alhaji Abdullahi Yusuf, ya yi kira ga shugabannin manyan tashoshin motoci a garuruwan Arewa su rika sanya ido sosai wajen hana dauko mutane cunkushe a tirela wanda hakan ke haifar da firgici ga al’ummar Yarbawa da ke Kudu.

“Ya kamata mahukuntan Arewa su dauki matakin hana wadannan abubuwa kwata-kwata domin kyautata tsaro da zamantakewarmu da mutanen wannan sashe,” inji shi.

Da yake yi wa ’yan jarida bayani a kan kama mafarautan, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ekiti ASP Sunday Abutu ya tabbatar da kama mutum 13 da suka hada da: Abubakar Ali da Salisu Isa da Musa Okasa da Yusufa Sani da  Abu Magaji da Umar Magaji da  Adamu Shehu da  Umar Shafi’u da Sale.  Sai kuma Musa da Mustapha Usman, da Musa Isa da  Muntaka Wada da kuma Usman Abubakar, wadanda ya ce an kama su ne a garin Emure-Ekiti a ranar Juma’a da ta gabata.

Ya ce, al’ummar garin ne suka kai rahoton bullar mutanen ga ’yan sanda wadanda suka hanzarta isa garin suka kama wadanda ake zargin.

Ya ce an same su da karnukan farauta guda 10 da adduna da wukake da bindigogi harbi-ruga da wasu layu da guraye.

Mutanen da aka kama sun yi bayyana cewa, sun fito ne daga Jihar Kano domin yawon farauta a yankin. Ya ce, za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.