✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kama mutum 123 a Legas ta tada kura . Rayuwar ’yan acaba a Legas

Kama mutum 123 a Legas ta tada kura . Rayuwar ’yan acaba a Legas   Yadda lamarin ya faru A safiyar Juma’ar makon jiya ce…

  • Kama mutum 123 a Legas ta tada kura . Rayuwar ’yan acaba a Legas

 

Yadda lamarin ya faru

A safiyar Juma’ar makon jiya ce jami’an tsaron hadaka na Legas  da ake kira tasfos suka kama ’yan Arewa 123 ’yan ci-rani da suka zo daga Jihar Jigawa cikin wata tirela dauke da baburan acabarsu 48. Jami’an sun kama su ne a Unguwar Agege tare da taimakon Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Kola Ogunjobi, lamarin da ya janyo cece-kuce.

Shugaban tasfos din ya bayyana cewa al’ummar gari ne suka ankarar da su, “Lura da halin tsaro da ake ciki a kasar nan musamman yadda ’yan bindiga suka addabi wasu jihohin kasar nan. Wannan ne ya sa mutane jihar suka tsorata ganin yadda suka shigo su 124  cikin tirela daya tare da babura 48 kuma sun boye kansu a karkashin tamfol. Da muka samu bayanai sai muka tare su a yankin Agege muka kawo su babban ofishinmu da ke Oshodi inda muka sauko da su daya bayan daya don tabbatar ba sa dauke da wani mugun abu. Da muka tabbatar ba sa dauke da komai sai baburansu, sai muka shaida wa jama’a ba sa dauke da wani mugun abu. Mun yi amfani da ’yan jarida ne muka nuna su domim jama’a su gane wa idonsu gaskiyar lamarin ba kamar yadda suka zata a baya ba, inda wadansu ke tunanin ko miyagu ne suka shigo gari don tada hankalin jama’a. Daga na sai Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta karbe su ta tantance su, bayan ta tabbatar ba masu laifi ba ne sai ta sake su,” inji shi. Ya kara da cewa ana ci gaba da bincike kafin a saki baburansu 48.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, DSP Bala Elkana ya ce “Rundunar ta bincike su ba ta same su da laifin komai ba, hasali ma da dama a cikinsu a Legas suke zaune da iyalansu, sun dawo Legas ne bayan sun je Arewa don yin Babbar Sallah, wadansu kuma sun shigo Legas ne a karon farko, mun sallame su bayan da muka tabbatar ba masu laifi ba ne.”

Kama mutum 123 ya janyo kace-nace musamman a kafafan sada zumunta na zamani inda wadansu  a ciki da wajen Legas suka nuna bacin rai ganin yadda aka kama mutanen aka kira su da bakin haure aka kuma gabatar da su ga manema labarai tamkar masu laifi.

Wadansu ’yan Arewa kamar  lauyan nan Audu Bulama Bukarti da dan jarida Ja’afar Ja’afar sun yi rubutu kan lamarin, haka kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Dutse a Jihar Jigawa ta nuna bacin ranta kan lamarin inda ta ce tauye hakki ne da ya saba Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan. Kuma ta jinjina wa Gwaman Jihar  Alhaji Muhammadu Badaru bisa kokarinsa a kan lamarin

Wadanda aka kama na neman diyyar Naira biliyan daya

Tuni wasu lauyoyi a karkashin jagorancin Lauya Abba Hikima suka shigar da Gwamnatin Jihar Legas kara a madadin ’yan ci-ranin 123 a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, inda suka bukaci a biya su diyyar Naira biliyan daya

Wadanda ake karar kamar yadda takardar karar mai lamba FHC/L/CS/1519/19 ta nuna, sun hada da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas, Zubairu Mu’azu, da Shugaban tasfos Yinka Ebgeyemi da Kwamishinan Shari’a na Jihar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton mahukuntan Jihar Legas ba su saki baburan ba, inda ake ci gaba da rike su a ofishin Hukumar Tasfos, lamarin da ya sanya wadansu ke yada jita-jitar cewa Gwamnatin Legas ta kwace su kuma za ta nike su kamar yadda ta saba yi a baya. Amma Kakakin Hukumar Tasfos ya bayyana wa Aminiya cewa ana ci gaba da bincike ne kafin a bai wa masu su kayansu

Wakilin Aminiya ya tuntubi Sarki Sani Kabiru daya daga cikin shugabanin ’yan Arewa mazauna Legas wanda ya tsaya wa mutum 123 da ’yan sanda suka sallama, inda ya ce ya za a bai wa mutanen baburansu 48. Ya ce a ranar Litinin da ta gabata Kwamishinan ’Yan sandan zai ba da umarni a ba su baburansu inda ya nemi wakilin Aminiya ya zo ofishin rundunar ’yan sandan domin ya shaida lokacin da za a ba su, amma da wakilinmu ya ziyarci ofishin, Sarki Sani Kabir ya  ce Kwamishina Zubairu Mu’azu ya yi tafiya zuwa  Jihar Oyo don halartar taro da Sufeto Janar kan zaman lafiya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a ba su baburan ba.

Ra’ayin ’yan Arewa mazauna Legas ya rabu biyu

Ra’ayin al’ummar Arewa mazauna Legas ya rabu biyu kan lamarin. Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu ya nuna takaici kan  faruwar lamarin inda ya ce bai kamata ba yadda ake zaune a matsayin kasa daya a kama mutane a kasarsu a kira su bakin haure har a gabatar da su ga ’yan jarida tamkar masu laifi. Ya ce halin kuncin talauci da rashin zaman lafiya a wasu sassan jihohin Arewa ne ya sa ’yan ci-rani ke tururuwar zuwa Kudu  inda y ayi kira ga gwamnatocin Arewa su tashi tsaye wajen bai wa al’ummarsu ilimi da samar wa matasa ayyukan dogaro da kai.

Shugaban ’Yan Arewa Na Jam’iyyar APC a Jihar Legas Alhaji Muhammadu Dandamma ya shaida wa Aminiya cewa tsare mutanen ba wani abu ba ne na tada hankali lura da yanayin da suka shigo Legas cikin ayari tare da baburn 48. “A wannan hali na rashi tsaro a wannan kasa ko jihohinmu na Arewa suka nufa irin wannan hali sai an tsare su an bincike su, don haka ban ga laifin gwamnati ko jami’an tsaro ba domin aikinsu suka yi na kiyaye al’umma baki daya. Sun tsayar da su sun bincike su bayan haka an sallame su. A ganina wannan bai kai a ce an kai karar gwamnati ba, mun san masu yin haka sun yi ne domin nuna kishinsu ka ’yan uwansu amma muna fata za su janye karar domin mu ’yan Arewa mazauna Legas mun samu fahimtar juna sosai da gwamnatin, mun muka yi ruwa-da- tsaki an sallame su,” inji shi.

 

Rayuwar ’yan acaba a Legas

Aminiya ta zagaya cikin garin Legas domin ganin halin da masu sana’ar acaba ke cikin musamman wadanda kan zo daga Arewa. Malam Abdulkadir Muhammad  ya ce ya yi shekara 20 yana sana’ar acaba a Legas. Ya ce a yanzu masu sana’ar suna cikin halin kunci lura da yadda jami’an tsaro ke farautarsu tamkar masu laifi. Ya ce daga Jihar Zamfara yake kuma yana da mata biyu da ’ya’ya 4 baya ga iyaye da ’yan uwansa da yake taimakawa. Ya ce daya daga cikin kalubalensu shi ne jami’an tsaro na tasfo ko kuma ’yan sanda domin duk wanda suka kama babu makawa sai ya biya Naira dubu 10 zuwa dubu 15.

Shi ma Nasiru Adamu dan acaba ne a Legas, ya ce zuwa yanzu jami’an tsaron Legas sun kwace masa babur guda uku, kuma sun tafi har abada. Ya ce akwai wanda sai da ya bai wa jami’an Naira dubu 20 don a saki babur dinsa amma bai fito ba. Ya ce baya ga kalubalen ’yan sanda, ’yan acabar na fuskantanr kalubalen muhali ko wajen kwana, “Ni dai na dade, ina da dakin da na kama haya, wadansunmu da ke da karfi suna kama dakin haya wadansu mutum uku, wadansu hudu har shida ko takwas sannan akwai dakin Naira dubu biyar zuwa shida a unguwannin masu saukk kuma akwai mutanen da idan sun sayi gidaje kafin su gyara su shiga suna bai wa mutanenmu su zauna. Domin akwai wani gida da wani mutum ya saya akwai sama da ’yan acaba 200 da ke kwana a ciki, sai dai akwai ’yan iskar gari da ke takura mana, ko da mun sayi kati, sai sun karbi kudin banza a hannunmu.” Ya kara da cewa “Idan muka dauki fasinja a gabansu, a kullum akalla mutum ya sayi katin Naira dubu, kuma an hana mu bin manyan tituna kuma mana kokarin kiyayewa amma har lungunan da muke aiki jami’an tsaro ke bin mu suna kwace mana baburanmu a wani lokacin ma suna shiga gidajen da muke kwana su kwashe mana babura. Don haka bukatarmu ita ce gwamnati ta shiga lamarin.”

 

Abin da ya sa muka shigar da kara – Barista Abba Hikima

Daga Isiyaku Muhammed

Da Aminiya ta tuntubi jagoran lauyoyin da suka shigar da karar, Barista Abba Hikima, ya ce kwace musu babura da aka yi tamkar fashi da makami ne.

“Abin da aka yi wa ’yan uwanmu na Jigawa a Legas, ya saba wa Sashi na 34, 35, 41 da 44 na Kundin Tsarin Mulkin Kasa. Legas ba wata kasa ba ce ballantana a ce sai an wulakanta mutane don za su shige ta. Laifi ne a sa su cire takalmansu, a jera su a gaban kyamara kamar wadansu masu laifi. Laifi ne a kwace musu babura tun kafin su hau baburan a Legas ballanata a ce sun karya dokar hana acaba. Laifi ne a tsare su fiye da awa 24. Laifi ne kuma kabilanci ne a tsangwame su ko a sawwaru su da ’yan Arewa. Idan mutum laifi ya yi kawai ka yi masa hukunci a matsayinsa na dan Adam ko dan Najeriya. Laifi ba ya da kabila,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Za mu ci gaba da bibiyar hakkinsu insha Allah har zuwa karshen shari’ar. Kuma ba ma neman komai daga hannunsu.”

Da Aminiya ta tambaye shi game da cewa idan aka yi la’akari da matsalar tsaro ko Gwamnatin Legas na da ikon kama su? Sai ya ce, “Ai dama kama su a karon farko ba laifi ba ne, idan akwai madogara kwakkwara a kan zargin da ake yi musu. Matsalar ita ce bayan an kama su da ’yan awanni aka tabbatar ba masu laifi ba ne amma aka ci gaba da tsare su har sama da awa 24. Sannan an ce an kwace musu babura saboda an hana acaba a Legas tun kafin su hau baburan nasu. A doka niyya kawai ba ta tabbatar da laifi, sai an aikata laifin da jiki tukunna ya zama laifi. Ma’ana sai abin da ake kira Actus Reus da Mens Rea sun hadu. Saboda haka kwace musu baburan da aka yi ba ya da bambanci da kwacen da ’yan fashi suke yi wa mutane a dokance.”