✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kama ’ya’yan PDP a Kaduna ya jawo cece-kuce

Ranar Talatar da ta gabata ce Jam’iyyar PDP ta zargi Jam’iyyar APC da jami’an tsaro da hada baki wajen musguna wa’ya’yanta ta hanyar kama su…

Ranar Talatar da ta gabata ce Jam’iyyar PDP ta zargi Jam’iyyar APC da jami’an tsaro da hada baki wajen musguna wa’ya’yanta ta hanyar kama su ana tsarewa a Jihar Kaduna.

Jami’an tsaro sun kama tare da tsare manyan ’ya’yan Jam’iyar PDP a jihar bisa zarginsu da yin kalaman tunzura jama’a da ka iya kawo rikici a lokacin zabe.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka ruwaito Daraktan Watsa Labarai na yakin zaben PDP a jihar Mista Ben Bako, yana cewa a hallaka duk wanda bai zabi PDP ba a Kudancin Kaduna.

Haka shi ma tsohon Shugaban Jam’iyar PDP ta Jihar Kaduna Alhaji Yaro Makama ana zarginsa da yin kalaman tunzura jama’a a lokacin yakin neman zabe a Lere.

Sai dai Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna Felid Hyet ya zargi gwamnatin APC da jami’an tsaro da hada baki domin musguna wa ’yan adawa.

Ya ce kame da cin zarafinsu ba zai hana su cin zabe ba.

Shi ma da yake mayar da martani a kan kama ’ya’yan PDP da aka yi, Shugaban Jam’iyyar APC Emmanuel Jekada yaba wa jami’an tsaro ya yi a kan kama wadannan mutane da suka yi saboda kalaman tunzura jama’a.

“Mun yi Allah wadai da Jam’iyyar PDP kan rashin yin Allah wadai da kalaman da shugabanninsu suka yi na neman a yi rikici a lokacin wannan zaben duk kuwa da cewa sun yi kalaman ne a bidiyo.”

Ya ce irin wadannan kalamai na ’ya’yan PDP ya nuna cewa ba a shirye suke a yi zabe mai inganci ba a cikin kwanciyar hankali da lumana.

A martanin da Hukumar Tsaron Kasa (SSS) ta yi kan dalilan kama Ben Bako, ta ce jami’an tsaron SSS sun gayyace shi ne domin ya zo ya yi karin bayani a kan kalamansa da ya yi wanda aka nada a bidiyo.

Hukumar ta ce da zarar sun kammala bincikensu za su gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.

Hukumar ta tabbatar wa jama’ar jihar cewa hukumomin tsaro za su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyinsu a lokacin zaben, don haka ta gargadi dukan masu yin kalaman tunzura jama’a su kauce wa yin haka don samun zaman lafiya a lokacin zaben da bayansa.