Da Dumi Dumi

Kamfani ya tilasta ma’aikatansa cin kifi mai rai da shan jinin kaji

Wani kamfanin saye da sayarwa da ke Guizhou, a kasar China, ya ladabtar da ma’aikatansa ta hanyar tilasta musu cin kifi mai rai da shan jinin kaji saboda rashin cika sharuddan aiki da suka yi wa kamfanin.

Rahoto ya ce, wannan mummunar ladabtarwa da aka yi wa ma’aikatan shagon sayar da kayan gini na Guizhou, ta janyo muhawara a shafukan Intanet lokacin da aka wallafa bidiyon ladabtar da ma’aikatan. Bidiyon ya nuna yadda wani ma’aikaci yana ciro kifi mai rai yana mika wa ma’aikatan yana umartarsu da su ci shi da ransa. Sannan bidiyon ya nuna wadansu kuma suna shan jini wanda ake kyautata zaton jinin kaji ne. A cikin rahoton an nuna cewa Kakakin Kamfanin na cewa, ma’aikatan ne suka sa kansu a aikin ba tare da wani ya tilasta musu ba.

Wani wakilin kamfanin da ake sayar da kayan ginin gidaje ya bayyana wa jaridar China ta Beijing News, cewa wannan ladabatarwa ta rutsa da ma’aikatan kamfanin 20 wadanda suka gaza sayar da hajjar kamfanin a rubu’in shekara, sannan su ma’aikajtan ne suka kirkiri wannan hanyar ladabtarwa ta hanyar cin kifi mai rai da shan jinin kaji, suka ce hakan da suka yi zai kara musu kaimi wajen zage damtse don cika burin kamfanin a nan gaba.

A wani rahoto da jaridar The South China Morning Post ta wallafa na goyon bayan wannan ladabtarwa, sai dai ta ce mafi yawan ma’aikatan sun mallaki shaguna kuma su ke ladabtar da kansu ta hanyar cin kifi mai rai tare da shan jini, sai dai hakan bai gamsar da masu bibiyar shafukan sadawarwar ba.

ADVERTISEMENT

Bayan wallafa rahoton a bidiyo, wata tsangayar ’yan kwadago ta bayyana wa manema labarai cewa, ta fara binciken yadda abin ya faru, idan aka samu mai kamfanin ko manaja da bada umarnin ma’aikata su yi haka za a hukunta su yadda ya kamata.

Aikata wasu abubuwan ladabtarwa ga ma’aikata ya zama ruwan dare a kasar China duk da dokar kasar da ta gindaya na tanadar hukunci. A shekarun baya an samu wasu shugabannin  wasu kamfanoni suna ladabtar da ma’aikatansu ta hanyar umartarsu da cin tsutsa mai rai ko kyankyaso saboda sun gaza cimma bukatun kamfanin da suke aiki.

A kasar China masu sharhi a shafukan sada zumunta na sukar wadanda suka mallaki kamfanoni saboda yadda suke ladabtar da ma’aikatansu kuma sun bukaci hukumomi su dakatar da aukuwar hakan nan gaba.

 

 

Share