Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kamfanin 9Mobile ya kyautata wa abokan huldarsa

Lubabatu I. Garba, KanoKamfanin Sadarwa na 9Mobile ya raba kyaututtuka ga abokan cinikinsa da ke Arewacin kasar  nan a wani bangare na bikin murnar cikar kamfanin shekara goma da kafuwa.

Bikin bayar da kyaututukan da aka yi wa take da “9mobile Northern Promo” an gudanar da shi ne a Kano inda aka bayar da babbar kyauta ta Naira miliyan daya ga wani matashi mai suna Usman Adamu Usman.

ADVERTISEMENT

Sauran wadanda suka samu kyaututtukan manyan wayoyin hannu sun hada da Kabiru Abubakar da Mamman Nebat da Sunday Oduwoyiye da Abdlhakim Abdullahi da saurasnu.

Da yake raba kyaututtukan ga wadanda suka yi nasara, Daraktan  Sashen Ciniki na Kamfanin Shiyyar Arewa, Mista Tosin Olulana wanda ya samu  wakilcin Shugaban Sashen Ciniki na Arewa, Babangida Mukaddas ya ce, “Kamfanin nan ya yi haka ne don ya nuna godiyarsa ga abokan cinikinsa wadanda suke tare da shi tsawon lokaci. Ba don wadannan mutane ba da ba mu kai shekara goma a matsayinmu na kamfani da ke tsaye da kafafunsa ba.”

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa “Kyaututtukan da abokan cinikin kamfanin za su iya samu sun hada da kyautar katin waya a kullum da kuma wayoyin hannu da kuma kudi haka kuma ana gaba ma mun tanadi mota sabuwa ga mai rabo daga cikin abokanan huldarmu.”

A cewar Babagida Mukaddas, “Ba wannan ne na karshe ba, akwai sauran dama har kashi biyu da za mu ba abokan cinikinmu damar shiga tsarin neman kyaututtukan tun daga yanzu har zuwa watan Afrilu. Abin da kawai mutum yake bukata shi ne ya mallaki layin kamfanin tare da sanya katin waya na akalla Naira 100 tare da aika sakon WIN ga lambobin 476 don samun damar shiga gasar.

Daraktan ya yi albishir ga abokan cinikinsu inda ya ce kamfanin ya kara inganta ayyukansa inda ya fito da sababbin tsare-tsare don jin dadin abokan cinikinsa.

Ya bayyana cewa Kamfanin 9Mobile yana da tsare-tsare da yake tallafa wa al’umma musamman ta fuskar abin da ya shafi ilimi, inda ya ce a yanzu haka  kamfanin ya dauki Makarantar Mata ta GGC, Dala inda Kamfanin yake gudanar da wani aiki ga makarantar duk shekara.

A jawabin godiya, wanda ya samu kyautar Naira miliyan daya, Usman Adamu Usman ya ce duk da cewa ya dade yana hulda da Kamfanin 9Mobile, bai taba zaton zai samu wannan gwaggwabar kyauta ba, “Gaskiya na yi matukar farin ciki da samun wannan kyauta da na yi don ban taba tsamanninta ba. Ga shi a matsayina na matashi na samu wannan kudi masu yawa. Ina mika godiyata ga wanann kamfani tare da yi musu fatan  alheri,” inji shi.

Jihohin da kamfanin ya sanaya cikin tsarin bayar da kyaututtukan sun hada da Kano da Jigawa da Katsina da Adamawa da Taraba da Bauchi da Gombe da Borno da kuma Yobe.