✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin AJINO MOTO ya nada Maryam Booth Jakadiyarsa a Arewa

Kamfanin West African Seasoning Company Limited  (WASCO) da ke yin sinadarin girki na AJINO MOTO, ya nada fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Maryam Booth a matsayin…

Kamfanin West African Seasoning Company Limited  (WASCO) da ke yin sinadarin girki na AJINO MOTO, ya nada fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Maryam Booth a matsayin Jakadiyarsa a Arewacin Najeriya.

Manajan Daraktan Kamfanin Mista Niki Junich ya ce duk da cewa sindarin girkin ya shiga kasuwannin kasar ne nan kimanin shekara 30 da suka gabata, amma an fara amfani da shi ne tun a 1909 a wasu kasashen inda yanzu yake da rassa 130 a kasashen duniya daban-daban.

Ya ce baya ga farin garin sinadari da kamfanin ke yi tuni kuma ya fito da  sinadarin Ma dish don biyan bukatun abokan huldarsa. “Yana kan gaba wajen samar da ingantacce  sinadarin girki wanda aka sarrafa shi da sinadarin Amino Acid da jikin dan Adam ke bukata don samun karin kuzari da lafiya,” inji shi. Mista Junich ya ce fiye da kashi 70 na kasuwancin sinadarin dananon yana fitowa ne daga Arewacin kasar nan.

Da yake karin haske game da dalilin zabar Maryam Booth da kamfanin ya yi a matsayin Jakadiyarsa, Shugaban Kamfanin ya ce lura da cewa jarumar  tana da dubban masoya ne ya sa suke son yin amfani da ita wajen janyo hankalin masoyanta da sauran al’ummar kasar nan don rungumar sinadarin girkin da kamfanin ke samarwa tare da bai wa kamfanin kariya daga masu kwaikwayo ko yin jabunsa.

A jawabinta yayin da take rattaba hannu a kan yarjejeniyarta da kamfanin, Jaruma Maryam Booth ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin al’ummar Arewacin Najeriya sun kara karbar sinadarin girki na AJINO MOTO hannu bibbiyu.

“Za mu yi iya kokarinmu wajen ganin mun wayar da kan al’umma ta hanyar amfani da kafafen watsa labarai da na sadarwa kan amfani da wannan sinadari. Hakan zai ba mu damar kara fadada kasuwancin sinadarin ta yadda wadanda ba su amfani da shi za su fara tare da rike shi a matsayin sinadarin dandanon girkinsu daya tilo,” inji ta.