✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin CROWN FLOUR ya kaddamar da sabuwar taliya

Kamfanin Crown Flour Mill Limited (Olam Grains) ya kaddamar da sabuwar taliya mai suna Crown Pasta a kasuwannin Najeriya. Bikin kaddamawar wanda aka yi ranar…

Kamfanin Crown Flour Mill Limited (Olam Grains) ya kaddamar da sabuwar taliya mai suna Crown Pasta a kasuwannin Najeriya.

Bikin kaddamawar wanda aka yi ranar Laraba a Abuja, ya samu halartar masu ruwa da tsaki na a harkar.

Kamfanin na Crown Flour ya kasance ana damawa da shi a fagen sarrafa nau’ukan fulawa fiye da shekara 40 da suka gabata.

Kamfanin Olam Grains ne saye kamfanin Crown Flour Mill a shekarar 2010; sa’annan kuma likkafarsa ta ja gaba, bayan da ya saye kamfanin BUA a 2015. Yana daga cikin manyan kamfanonin da suka yi zarra a harkar sarrafa fulawa a Najeriya, inda yake sarrafa taliyar dafawa da kuma garin semobita da kuma fulawar hada burodi.

Da yake jawabi yayin kaddamawar, Mista Nitin Mehta, Shugaban Kasuwanci na kamfanin, ya jaddada kudurin kamfanin wajen gamsar da kwastomominsa a Najeriya. Misis Bola Adeniji, ita ce Shugabar Tallar Kamfanin, ta bayyana cewar taliyar tana da inganci sosai, kuma ba ta cabewa kuma tana dauke da sinadaren bitamin da dama, ga kuma farashi mai sauki.

Shi ma a nasa tsokacin a wajen taron, Mista Charles Babarimisa, Shugaban Cinikayya na kamfanin ya gode wa manyan dilolin da suka halarci kaddamar da taliyar wajen ganin sun tallafa ta fuskar hada kakkarfar alaka ta rarraba taliyar a sassan kasar.