✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Daily Trust ya ba Makarantar Marayu ta Jam’iyyar Matan Arewa kwamfutoci 10

Kanfanin Media Trust Limited, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya ba da tallafin kwanfutoci 10 ga Makarantar Marayu ta Jam’iyyar Matan Arewa da…

Kanfanin Media Trust Limited, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya ba da tallafin kwanfutoci 10 ga Makarantar Marayu ta Jam’iyyar Matan Arewa da ke Kaduna.

Kamfanin ya ba da kwanfutocin ne ga Sashen Koyar da Ilimin Kwanfuta na Makarantar domin inganta ilimin marayun da ke  makarantar.

Da yake mika kyautar ga hukumomin makarantar, Mataimakin Janar Manaja mai kula da Sashen Kwanfuta na Kamfanin Media Trust, Malam Garba Aliyu, ya ce an ba da kwanfutocin ne ga makarantar domin inganta ilimin dalibanta a fannin kwanfuta.

Ya shaida wa shugabannin makarantar cewa kwanfutocin masu tsada ne kuma na zamani don haka akwai bukatar su kula da su domin jin dadin marayun.

“Muna kuma fatar wadannan kwanfutoci kan tebur da na Laptop biyu da aka ba ku za ku kula da su da kyau tare da yin amfani da su wajen koyar da dalibanku a fannin kwamfuta,” inji shi.

Shugaban Sashen Kasuwanci na Kamfanin, Malam Abubakar Yusuf Jidda  wanda yana daya daga cikin ayarin ma’aikatan kamfanin da suka yi kai kwamfutocin zuwa makarantar ya yaba wa shugabannin makarantar kan yadda suke kula da marayun inda ya ce wannan na daga cikin dalilan da suka sa Kamfanin Media Trust ya ga sun cancanci a tallafa musu.

Ya yi fatan Allah Ya ci gaba da taimaka shugabannin makarantar domin su samu karfin gwiwar  ci gaba da taimaka wa marayun da suke hannunsu.

Mataimakiyar Sakatariyar Jam’iyyar Matan Arewa, Hajiya Amina Ladan-Baki ta ce makarantar daya ce daga cikin ayyukan marigayi Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello, wanda kuma Matan Arewa ke ci gaba da kulawa da ita.

“Muna mika godiyarmu ga Kamfanin Media Trust a bisa wannan abin alheri da ya dade yana yi mana. Domin kamfanin ya kwashe shekara kusan 10   yana taimaka mana. Muna kuma godiya a kan haka, Allah kumaYa  kara daukaka kamfanin,” inji ta.

A nata jawabin, Shugabar Makarantar Hajiya Maryam Ahmed Tahir cewa ta yi akalla marayu dubu daya ne makarantar ta yaye tun daga 1965.