✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Dana ya ki biyanmu diyya -Mazauna unguwar Iju-Ishaga

A yayin da ake gudanar da bikin juyayin tunawa da wadanda hadarin jirgin sama na kamfanin Dana ya rutsa da su a unguwar Iju-Ishaga da…

A yayin da ake gudanar da bikin juyayin tunawa da wadanda hadarin jirgin sama na kamfanin Dana ya rutsa da su a unguwar Iju-Ishaga da ke cikin jihar Legas masu gidaje da ’yan hayan da jirgin ya fada  a kan gidajensu sun zargi kamfanin da kin biyan su diyya.
Gungun mutanen wadanda suka kira kansu  ‘Ground bictims of Dana Air Crash’ wato jama’ar kasa da hadarin jirgin Dana ya rutsa da su sun nuna damuwa kan wulakancin da aka yi musu a wurin bikin juyayin wadanda suka rasu sakamakon hadarin.
Mai magana da yawunsu, mai suna Mista Gbenga Julius ya shaida wa manema labarai cewa, “Mu masu gidaje da ’yan haya wadanda jirgin ya fada a kan dukiyoyinmu da kadarorinmu mun yi asara mai dimbin yawa kuma mun shiga damuwa saboda asarar da muka yi, amma duk da asarar da muka yi gwamnati da kamfanin jirgin sama na Dana ba su sanya mu cikin wadanda za a ba diyya ba.
“Mun sami labari a kafafen yada labarai cewa gwamnati da kamfanin Dana sun biya wadansu diyya. Kun ga ai ba a kyauta mana ba, mu iyalai 19 da muka rasa dukiyoyinmu ba daya daga cikinmu da ya sami wani abu daga kudin diyyar da aka ce an biya. Shi ya sa muka yanke shawarar mu nemi lauya wanda zai bi kadinmu ya kwato mana hakkinmu daga wurin gwamnati da kuma kamfanin jirgin sama na Dana”.
Da yake jawabi, wani mutum da ya rasa ’yar uwarsa da danta a hadarin jirgin, mai suna Ndubisi Nwakalu, ya soki lamirin gwamnatin tarayya na rashin tabuka rawar a-zo-a-gani dangane da biyan su diyya.
Shi ma lauyan mutum 30 da hadarin ya rutsa da su, mai suna Mista Gbenga Eguntola ya soki yadda kamfanin jirgin sama na Dana ke aiwatar da lamarin biyan diyya ga dangin wadanda hadarin ya rutsa da su.
Shugaban sashen yada labarai na kamfanin Dana, mai suna Tony Usidamen ya ce tuni kamfanin ya biya diyya ga wasu daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su, amma an sami tsaiko a biyan wadansu saboda rashin cikakkun takardun shaida.
Ya bayyana cewa kamfanin na kan biyan wadanda hadarin jirgin ya rutsa da su a kasa, amma an sami cikas saboda doka ba ta bayyana yawan kudin da za ba su ba.
“Shi biyan diyya ya danganta da yawan asarar da aka yi. Ina mai tabbatar muku da cewa dangi uku tuni aka biya su diyyar ’yan uwansu a makon da ya gabata, bayan an cimma yarjejeniya. daya daga cikinsu ya sami Dala dubu 100. Ka ga shi Fasto Omaumi, wanda ya fi kowa yin asarar kadarori, an ba shi Dala dubu 30 duk da cewa ana ta tattunawa da lauyansa a ga yadda za a fahimci juna”. Inji shi.
Ministar zirga-zirgar jiragen sama, Princess Stella Adaeze Odua ta shaida wa manema labarai cewa an kafa kwamitin  da zai binciki tsare-tsare da lafiyar jiragen sama sakamakon hadarin jirgin Dana.
Ta ce tun shekarar da ta gabata, bayan hadarin, hukumar lura da zirga-zirgar jiragen sama ta NCAA take aiki kafada-da-kafada da kamfanin jirgin sama na Dana da kamfanonin Inshora da kuma gwamnatin Jihar Legas don ganin an gaggauta biyan diyya ga wadanda hadarin ya rutsa da su.