Da Dumi Dumi

Kamfanin  Jiragen Najeriya zai sami Naira Biliyan 47

Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe Biliyan 47 a cikin kasafin kudin Bana 2019 domin farfado da kamfanin jiragen samanata kamar yadda karamin Minista Hadi Sirika ya shaida wa manaema Labarai.

Ministan ya ce gwamnati za ta bunkasa kasuwancinta na jiragen sama ta hanyar zuba jari kafin daga bisani ta gabatar wa masu zuba jari.

Ganin yadda gwamnati ta himmatu wajen farfado da tsohon Kamfanin Jiragen samanta mai suna , ‘Nigeria Airways’ ta ware zunzurutun kudi har Naira Bliyan 47 domin saka jari a cikin  kamfanin, daga bisani ta gayyaci masu zuba jari.

Aminiya ta yi waiwaye a kan tsohon kamfanin na Najeriya. An kafa kamfanin Jiragen sama na Najeriya wanda aka fi sani da ‘Nigeria Airways’ a shekarar 1958, a da ana kiransa da suna ‘WAAC’ wato kamfanin jiragen sama na Afirika ta Yamma, kafin daga bisani a canza masa suna zuwa ‘Nigeria Airways’ a shekarar 1971  da wannan suna ya ci gaba da aiki har lokacin da ya durkushe a shekarar 2003. Kamfanin ya kasance Gwamnatin Najeriya tana da kashe 51% cikin dari na jarin Kamfanin kafin daga bisani a shekarar 1961, Najeriya ta mallaki kamfanin kashi 100%  wato ya zama mallakar ta.

Tun daga lokacin Jiragen suke zirga-zirga a yankin Afirika ta Yamma da Tarayyar Turai da Amurka da kasar Saudi Arabiya da kuma zirga-zirga a cikin gida. A wancan lokacin akwai kamfanoni da dama da suke gudanar da kamfanin wanda suka hada da Kamfanin Birtaniya (British Airways) da KLM na kasar Holand da kuma kamfanin  kasar Afirika ta Kudu.

ADVERTISEMENT

Kamfanin ya samu tagomashi sosai a farkon shekarar 1980, a wancan lokacin kamfanin Kasar Holand KLM shi ne, wanda Gwamnatin Najeriya tayi hayarsa domin ya kula da har kokin kamfanin Nigeria Airways kuma ya  samu tagomashi, inda sai da kamfanin ya mallaki Jirage guda 30 a wan can lokacin kamfanin ya bunkasa kuma ya mallaki manyan jirage ciki harda su Airbus A310, Boeing 737 da sauransu.

Sai dai bayan da kamfanonin kasashen waje suk janye daga Nigeria Airways sai kamfanin yashiga halin rashin tabbas, cin hanci da rashawa ya dabai-baye kamfanin da yawan ma’aikata da bashi wanda yakai Dalar Amurka $528,000,000 a wan can lokaci. Kafin durkushewar kamfanin Jirgi daya kacal ya rage masa wanda yake motsi acikin gida da kuma guda biyu ma su zuwa ketare. Daga karshe kamfanin Birgin Najeriya shine ya gaje tsohon kamfanin ‘Nigeriya Aiways’ shi kuma ‘Airk Air’ ya cigaba da amfani da kayayyakin kafanin wanda ake ce masa ‘ground Facilities’.

Abin jira agani shi ne ko kwalliya zata biya kudin sabulu ko kuma za a kuma gidan jiya, lokaci shine kadai zai zama alkali.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya