Da Dumi Dumi

Kamfanin Madarar Hollandia Ebap ya sake sabon mazubi

Domin sadar da abokan hulda da sabon ci gaba, kamfanin madarar Hollandia Ebap ya samar da wani sabon mazubi da zai kayatar da abokan hulda. Madarar Hollandia tana  daya daga cikin madara mafiya shahara a bangaren samar da gamsasshiyar madara a  Najeriya.

Sanarwar kamfanin ta ce shaidar da za a gani a jikin sabon mazubin ita ce ta launin shudin wanda yake nuna muhimmanci da sabon mazubi na zamani tare da launin gwal a jikin shaidar kamfanin. madara mai kayatarwa kuma abar karin kumallo.

“Madarar Hallandia Ebap tana dauke da sinadarai masu watsakarwa da masu gina jiki da za su kara wa jiki kuzari da kuma yanayi mai dadi,” inji sanarwar.

Manajan Daraktan Kamfanin Chi Limited da ke samar da madara,Mista Deepanjan Roy, ya ce abokan huldarsu da suka saba da tsohon mazubin Hollandia suna ba su tabbacin cewa amfani da sabon mazubin ba zai canja asalin dandanon madarar Hollandia da suka sani ba, sai dai sun ci gaba da inganta ta, ta hanyar samun sinadarai masu gamsarwa.

“Madarar Hollandia Ebap tana dauke da sinadarai da dandano mai gamsarwa, sannan tana nan a cikin mazubi mai karko da tsabta domin amfanin abokan huldarmu da kuma ajiyarta na wani lokaci. Tana da inganci da karko kuma ta dace da karin kumallo da za a iya hada ta da shayi da kunu  domin samun gamsuwa wajen karin kummalo,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ce sabon mazubin Hollandia ana iya samun mazubi mai giram 60 da giram120 da kuma giram190 kuma ana iya  samunta a shagunan Chi da kasuwanni da kuma kantunan unguwanni a sassan Najeriya.

 

Share