✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Media Trust ya karrama ma’aikatansa 41

A shekaranjiya Laraba ce Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya karrama  ma’aikatansa 41 wadanda suka kai shekara 15 da kuma…

A shekaranjiya Laraba ce Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya karrama  ma’aikatansa 41 wadanda suka kai shekara 15 da kuma wadanda suka kai shekara 10 suna aiki da kamfanin.

Haka kuma akwai wadanda aka karrama domin nuna Gaskiya da Rikon Amana (Integrity Award) da wadanda aka karrama kan Aikin Tukuru, da kuma wani jami’in tsaron kamfanin da aka karrama ta musamman domin nuna gaskiyarsa ta hanyar dawo da wasu kudi da ya tsinya.

Wadanda suka kai shekara 15 a kamfanin su 6, daga cikinsu akwai Editan Daily Trust ta ranar Asabar, Abdulkareem Baba Aminu, da Manajan Bangaren Tsara Shafuka, Hussaini Garba Mohammed, da Shugaba Sashen Cigaban Kasuwanci Hamisu Muhammed da Abdullateef Tiamiyu da Abbas Abiri dukkansu daga bangaren harkokin kudi.

A bangaren wadanda aka karrama wadanda suka kai shekata goma suna aiki, akwai Editan Tsara Shafuka da Labaran Wasanni na Aminiya, Ahmad Garba Mohammed da mai tsara shafuka, Stanley Bainta, da tsohon editan binciken kwa-kwaf Nuruddeen M. Abdallah da Banessa Adie Offiong da sauransu.

Wadanda aka karrama domin Gaskiya da Rikon Amana su ne Opeyemi Kehinde da Abubakar Saleem. Masu aiki tukuru kuma su ne, Manajan Kirkira na Kamfanin, Ali Ahmad Geidam da Haruna Ibrahim da Tiamiyu Abdullateef.

Sai shi kuma jami’in tsaron, Hamisu Hakuri wanda aka karrama na musamman saboda ya tsinci kudi ya zo ya shelanta cewa ya tsinci kudi, har aka gano mai shi aka mayar masa.

  Daga hagu Babban Daraktan Kudi da Zuba Jari na Kamfanin Media Trust Malam Nura Daura ne yake miqa wa Ahmed  Garba Mohammed na Aminiya lambar yabo
Daga hagu Babban Daraktan Kudi da Zuba Jari na Kamfanin Media Trust Malam Nura Daura ne yake mika wa Ahmed Garba Mohammed na Aminiya lambar yabo

Da yake jawabi a wajen bikin karramar, Babban Jami’in Zartarwa kuma Babban Editan Kamfanin, Malam Mannir dan-Ali, ya ce ana shirya bikin ne domin a karrama ma’aikata masu gaskiya da rikon amana da masu kokari wajen aiki. Sannan ya bayyana yadda kamfanin ke da ma’aikata nagartattu wadanda suka san aiki, musamman duba da yadda aka yi wa kamfanin ta’aziyyar rasuwar marigayi Bashir Liman da Shehu Abubakar.

Daga karshe sai ya bukaci ma’aikatan da suka ci gaba da dagewa wajen aikinsu, sannan ya bukaci iyalan wadanda suka zo taron da suka ci gaba da mazansu ko ’yan uwansu hadin kai wajen gudanar da ayyukansu.

A nasa jawabin, Shugaban Gudanarwar Kamfanin, Malam Kabir Yusuf cewa irin karramar yana nuna cewa Najeriya ba kasa ba ce ta batari, kasa ce da take cike da mutanen kirki masu nagarta

Sannan ya ce kamfanin zai ci gaba da karrama ma’aikatansa jajirtattu, inda ya ce baya ga biyan albashin da suke wanda ba su taba gazawa ba, ma’aikan kamfanin suma suna cikin wadanda suke cin moriyar ribar da aka samu, inda ake ware musu kashi biyar na riban da kamfanin ya samu.

Bikin karramawar, wanda aka yi a otel din Chida da ke Abuja, ya samu halartar dukan daraktoci da shugabannin kamfanin da kuma dimbin ma’aikata daga sassan kasar.