✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Media Trust ya samu lambar yabo daga Hukumar NACA

Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa, NACA, ta bayar da lambar yabo ga jaridun Daily Trust da kuma Aminiya, kan abin da ta kira…

Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa, NACA, ta bayar da lambar yabo ga jaridun Daily Trust da kuma Aminiya, kan abin da ta kira yadda jaridun suka yi zarra wajen da bayar da rahotannin da suka jibanci cutar ta kanjamau wato HIB.

Jaridun biyu sun yi nasarar lashe kyautar mai lakabin ‘National Response Support Category’ tare da takwarorinsu na NTA, da kuma jaridar Premium Times.

Sauran da suka samu karramawar su ne Shirin Shugaban Kasar Amurka ta Fuskar Rage Radadi ga masu Larurar Cutar ta HIB, PEPFAR’ a takaice, sai kuma Shirin Ci gaban Kasashe na Kasar Birtaniya watau DFID da kuma kamfanin wayar salula na MTN da dai sauransu.

Hukumar ta NACA ta ce an yi la’akari wajen ba Jaridar Daily Trust din wannan kyautar lura da yadda take isar da sakonnin ilimantar wa game da cutar zuwa ga miliyoyin ’yan Najeriya ta kafar jaridarta ta harshen Hausa wato Aminiya.

Da yake magana a karshen makon jiya a Abuja, Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire ya ce ko da shike kasar ta samu raguwa wajen yaduwar cutar, har yanzu ana samun sabbin wadanda suke kamuwa da cutar mai karya garkuwar jiki.

Sa’annan ya jinjinawa wadanda aka bai wa lambobin yabon sakamakon azamarsu wajen yaki da cutar a Najeriya har ya zuwa yanzu.

Ministan ya kuma kira ’yan Najeriya da su ci gaba da zuwa ana musu gwajin cutar domin sanin matsayarsu. Su kuma san ko suna dauke da kwayar cutar domin idan aka fahimci cewar kwayar cutar ba ta kai wani mataki ba, ba zai yiwu a iya yada shi ga wani ba.