✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Microsoft zai sayi wani sashe na kamfanin Nokia

Kamfanin Microsoft ya shiga wata yarjejeniya ta sayen wani sashe na wayar salula ta Nokia a kan kudin Euro sama da biliyan biyar. Shi kuma…

Jami’an kamfanin NokiaKamfanin Microsoft ya shiga wata yarjejeniya ta sayen wani sashe na wayar salula ta Nokia a kan kudin Euro sama da biliyan biyar. Shi kuma kamfanin na Nokia zai ba da lasisi da sha’anin taswirori ga Microsoft.
Yarjejeniyar dai ta sa darajar hannayen jarin kamfanin Nokia ya yi tashin gauron zabi da kashi 45 cikin dari.
A farkon shekarar 2014 ne ake sa ran kammala yarjejeniyar, a lokacin da kimanin ma’aikatan  kamfanin Nokia dubu 32 za su koma Microsoft.
Yayin da kamfanin Nokia yake fadi-tashi domin kamo abokan gogayyarsa irinsu Samsung da Apple, an soki kamfanin Microsoft da jan kafa wajen shiga kasuwar wayoyin salula.
Shugaban kamfanin Microsoft Stebe Ballmer, a wata sanarwa ya bayyana cewa, “Wani tsallan badake ne a kan makomarmu, kuma kowa zai ji dadi daga ma’aikata da masu jari a kamfanin da kuma masu sayen kayanmu.”
Yarjejeniyar na jiran amincewar masu hannun jari a kamfanin Nokia da kuma shugabannin gudanarwar kamfanin.
Masana na kallon yunkurin na kamfanin Microsoft, a matsayin tabbatar da cewa ya yi tsare-tsaren da suka dace domin shiga kasuwar wayoyin salula.
A baya wayar Nokia ce ke kan gaba a kasuwar wayoyin salula, amma daga bisani cinikin wayar ya fadi da kashi 24 cikin dari, a watanni uku zuwa karshen watan Yuni.
Sai dai cinikin waya samfurin Lumia da Nokia ke kerawa, wanda ke amfani da tsarin Microsoft ya karu a wannan lokacin.
Kamfanonin biyu sun kuma amince da lasisi na shekaru goma, wanda zai ba kamfanin Microsoft damar amfani da wayoyin Nokia a wayoyin salulan da yake samarwa.