✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin MTN ya shiga Kasuwar Hannun Jari ta Kasa

Kamfanin sadarwar wayar salula na MTN, a hukumance an kaddamar da shi cikin Kasuwar Hannayen Jarin Najeriya a jiya Alhamis, bayan da kamfanin ya cika…

Kamfanin sadarwar wayar salula na MTN, a hukumance an kaddamar da shi cikin Kasuwar Hannayen Jarin Najeriya a jiya Alhamis, bayan da kamfanin ya cika dukkan sharuddan da suka dace wajen shiga kasuwar, kamar dai yadda wasu jami’ai biyu na kamfanin suka tabbatar wa Aminiya.

Jami’an kamfanin na MTN da na Kasuwar Hannayen Jarin Najeriyar, wadanda suka bukaci a sakaya sunayensu, sun tabbatar mana cewar, hannayen jarin kamfanin sadarwar da suka kai Naira biliyan 20.3, za a fara hada-hada da su cikin makon nan mai karewa.

“Eh, ina mai tabbatar maka cewa mun fara hada-hada a kasuwar jiya’’ inji wannan babban jami’in MTN.

“Abin da zan iya cewa a nan shi ne, ‘yan Najeriya masu zuba jari sun fara hada-hada da kamfanin na MTN a makon nan,” kamar yadda wani jami’i a Kasuwar Hannayen Jarin Najeriya ya shaida wa Aminiya.

A makon jiya, katafaren kamfanin sadarwan ya fadi cewa ya kamalla rajistar hannayen jarin Naira biliyan 20.3 a kan Kwabo 0.02 da Hukumar Hada-Hadar Hannayen Jari ta kasa.

Kamfanin ya ce nasarar wannan rajistar ce ta sanya a makon nan ya samu damar shiga sahun masu hada-hadar hannayen jari da Kasuwar Hannun Jarin Najeriya.

Babban jam’in gudanarwar Kamfanin, Ferdi Moolman, ya bayyana cewa: “Ina matukar farin ciki da kai wa wani gwadabe a kokarinmu na shiga kasuwar hannayen jarin. Kuma muna isar da godiyarmu ga Hukumar kula da Hannayen Jari ta kasa (NSE) da ma Hukumar Yi Wa kamfanoni Rijista (CAC) a kan irin dafa mana da suka yi, ta fuskar hakan.”

Kamfanin wanda mallakin kasar Afirka ta Kudu ne, a watan jiya ne ya bayyana cewa, zai rikida daga kamfani mai zaman kansa zuwa kamfani na jama’a.

Mista Moolman ya ce shigar kamfanin kasuwar hannayen jarin Najeriya zai ba da damar samun wasu sabbin masu zuba jari tare da bude kofa ga ‘yan Najeriya da dama, a dama da su a jarin kamfanin.

Ya kuma nuna cewa, hakan ya jaddada dadadden kudurin kamfanin na bunkasa jarin kamfanin don ‘yan Najeriya su ci gajiyarsa tare da samun ayyukan kamfanin a kodayaushe.