✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Nike ya fito da sabuwar kwallon gasar Premier ta Ingila

Shahararren kamfanin nan da ke sayar da kayayyakin wasanni mai suna Nike a shekaranjiya Laraba ya fitar da sabuwar kwallon da za a yi amfani…

Shahararren kamfanin nan da ke sayar da kayayyakin wasanni mai suna Nike a shekaranjiya Laraba ya fitar da sabuwar kwallon da za a yi amfani da ita a kakar wasa ta bana a gasar rukuni-rukuni ta Ingila.
Kamfanin ya ce ya fito da sabuwar kwallon ce don jin dadin ’yan wasa da alkalan wasa da kuma daukacin ’yan kwallo.
Kamfanin ya ce ya rage wa kwallon nauyi kuma za ta rika yawo a iska ba tare da matsala ba sannan ’yan kwallo ba za su rika gajiya da wuri ba idan suna lailayata.
Haka kuma kwallon za ta rika ba ’yan kwallo damar jefa ta a raga cikin sauki walau suna kusa ko nesa da raga. Haka kuma masu tsaron gida watau gololi za su samu saukin tare ta da zarar an narko musu kwallo.
Tuni Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Ingila (FA) ta amince da kwallon inda ta sanar da kungiyoyin kwallon kafa da za su fafata a gasar ta Premier a bana a kan canjin da aka samu na amfani da sabuwar kwallon.