Kamfanin suga na jahar Jigawa da ke Hadejia da aka gina tun zamanin tsohon gwamnan jahar Alhaji jihar Jigawa Ibrahim Saminu Turaki wanda iyalan marigayi Janar Sani Abacha suka saya zai fara aiki a shekarar 2015.
Iyalan marigayin sun ziyarci kamfanin kwanan nan inda suka bayyana cewa za a bude kamfanin ne da nufin samar wa matasa aikin yi a yankin masarautar Hadejia da kuma jahar Jigawa baki daya.
Gwamnatin Sule Lamido ce ta sayar da kamfanin ga iyalan marigayi Sani Abacha kasancewar ita gwamnatin jahar ba za ta iya cigaba da gudanar da kamfanin ba.
Daraktan sahin kere-kere na kamfanin Malam Umar Sanda ne ya sanar da manema labarai haka a lokacin da suka ziyarci kamfanin.
Malam Sanda ya kara da cewa, tunda iyalan marigayi Abacha suka mallaki kamfanin ba su ziyarce shi ba saboda abin da suka kira rubabbun injina da ke kamfanin, abin da ya zame wa iyalan marigayin dole su samar da injina masu inganchi don ganin kamfanin ya soma aiki gadan-gadan domin yin gogayya ga sauran takwarorinsa dake fadin kasar nan.
Ya kara da cewa, hukumar kula da kogin Jama’are da Hadejia za ta bai wa kamfanin hekta 4000 da zai dasa irin rake, kuma da zarar kamfanin ya fara aiki zai dauki ma’aikata 756 na wuccin-gadi a bangarori daban-daban na kamfanin.
Haka kuma zai dauki mutane kamar 2,500 ‘yan asalin yankin masarautar Hadejia aiki da kuma wadanda ba ‘yan jahar ba.
Kamfanin suga na Hadejia zai fara aiki a shekarar 2015
Kamfanin suga na jahar Jigawa da ke Hadejia da aka gina tun zamanin tsohon gwamnan jahar Alhaji jihar Jigawa Ibrahim Saminu Turaki wanda iyalan marigayi…