Da Dumi Dumi

Kamfanoni 40 suka nemi kwangilar gyara da samar da kadada 2,411 a Kano da Jigawa – Jami’i

Alhaji Mustapha Baba Shehuri Minista a Ma’aikatar Gona ta Tarayya
Alhaji Mustapha Baba Shehuri Minista a Ma’aikatar Gona ta Tarayya

Kimanin kamfanoni 40 ne suke neman kwangilar aikin gyara tare da samar da kadada 2411 da kuma samar da hanyar da za ta hada manoma da kasuwanni mai tsawon kilomita 80 a jihohin Kano da Jigawa.

Ko’odinetan Shirin Gwamnatin Tarayya kan Farfado da Ayyukan Gona (ATSAP-1) a Jihar Kano, Malam Ado Shehu ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce an kirkiro shirin ne don samar da aikin yi da karuwar arziki ta hanyar farfado da ayyukan gona tare da samar da wadataccen abinci a kasa.

Malam Ado ya nanata cewa shirin ya samar da shirye-shiryen kai-dauki masu yawa wadanda suka taimaka tare da ciyar da harkar aikin gona gaba.

A cewarsa shirin zai hada kai da Bankin Raya Afirka wajen ginawa da gyara kadada 1141 a Jihar Kano da kadada 1270 a Jihar Jigawa, “Wannan aiki za a yi shi ne a kananan hukumomi 11 a jihohin Kano da Jigawa. Shirin zai bunkasa ayyukan gona a jihohin biyu yadda za a samu abinci mai inganci tare da samar da kasuwa ga manoma don sama musu riba a nomansu. Har ial yau ayyukan noma za su samu ci gaba yadda za a sauya daga noman ci-da-kai zuwa noma don riba,” inji shi.

ADVERTISEMENT
Share