Search
Subscribe
Kamfanoni sama da 400 suka halarci Kasuwar Baje Koli ta Jos

Kamfanoni sama da 400 suka halarci Kasuwar Baje Koli ta Jos

Kamfanoni sama da 400 suka halarci Kasuwar Baje Koli ta Jos

Shugaban  Kungiyar masu Masana’antu da Aikin Gona da Ma’adanai ta Jihar Filato, Mista Bulus Dare ya ce kamfanoni da masana’antu da ’yan kasuwa daga ciki da wajen Najeriya sama da 400 ne suka baje kolin kayayyakinsu a Kasuwar Baje Koli ta Jos da kungiiyar ta shirya.

Mista Bulus Dare ya bayyana haka ne aokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a Jos inda ya ce kamfanoni da masana’antu da ’yan kasuwa da sauran jama’a daga ko’ina a Najeriya da kasashen Senegal da Nijar da Ghana da Habasha da  Mali da Bangaladesh sun zo kasuwar Baje Koli ta Jos, sun baje kayayyakinsu.

Ya  ce babu shakka an samu babbar nasara bana domin an gudanar da wannan kasuwa lafiya, kuma dukkan bakin  da suka halarci kasuwar kowa ya koma lafiya.

Wani dan kasuwa daga kasar Sudan da ya halarci kasuwar, mai suna Dokta Muhammad Sudan ya shaida wa wakilinmu cewa ya kawo kayayyakin turare na mata ne kasuwar.

Ya ce suna hada wannan turare ne da itatuwan kasar Sudan, inda ya ce  sau biyar ke nan yana zuwa Kasuwar Baje Koli ta Jos.

Ya ce a bana Kasuwar Baje Kolin,  babu ciniki saboda halin da ake ciki na rashin kudi.

Wata ’yar kasuwa da ta fito daga Jamhuriyyar Nijar mai suna Hajiya Zainab Nijar, ta ce ta kawo  turaren wuta da sabulai na mata ne. Ta ce a bana babu ciniki saboda halin da ake ciki. Amma akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasuwar.

Ta ce ana zuwa Kasuwar Baje Koli ce domin a hadu da juna a  kulla harkokin ciniki don haka ko babu  ciniki akwai alfanu. Domin dan kasuwa zai hadu da abokan ciniki ko bayan kasuwar.

Ta ce ta saba  zuwa kasuwannin baje koli irin wadannan a kasashen daban-daban na Afirka da Turai.

Shi ma wani dan kasuwa daga Kano mai suna Alhaji Aminu  Danjirgi Maiyadi, ya ce ya kawo yadidduka da atamfofi da leshi da shadda ne zuwa kasuwar.

Ya ce kasuwar ba ta taba cika irin na bana ba, saboda zaman lafiyar da aka samu. Amma  kuma ba ta taba rashin ciniki irin na bana ba.

A zantawarsa da wakilinmu wani dan kasuwa daga Kano mai suna Alhaji Sadik Musa, ya ce ya kawo dan kunne ne, inda ya ce bana mutane suna kukan rashin kudi,  saboda haka ba su iya sayen ’yan kunne da suka kawo ba, duk da rage farashinsu da suka yi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin