✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanonin Royal Edclusibe da WACL sun bude shagon kayan gini a Sakkwato

Dillalan kayan gini a Jihar Sakkwato sun yaba wa kamfanin kayan gini na West African Ceramics Ltd da ROYAL Brand bisa fito da tsarin katafaren…

Dillalan kayan gini a Jihar Sakkwato sun yaba wa kamfanin kayan gini na West African Ceramics Ltd da ROYAL Brand bisa fito da tsarin katafaren shagon kaya na Royal Edclusibe Showroom a jihar.

Sun bayyana jin dadinsu ne a lokacin da ake kaddamar da sabon shagon kayayyakin ginin a Layin Sheikh Abdulrahman Sudais da ke Sakkwato.

Wata sanarwa daga Kamfanin WACL, ta bayyana cewa hadakar an yi ta ce domin karfafa wa gwamnati wajen habaka bangaren da kuma bunkasa kayayyakin cikin gida.

“Wannan tsarin zai taimaka wajen samar wa magina da masu gini da sauran masu ruwa-da- tsaki a harkokin gini hanyoyin rage asara da samun sauki da samun kaya cikin sauri,” inji sanarwar.

Da yake jawabi lokacin kaddamar da shagon kayayyakin ginin, Manajan Darakta na Kamfanin Ribalka Nig. Ltd Alhaji Ribado Aliyu ya ce wannan tsari shi ne na farko a Jihar Sakkwato, kuma a cewarsa zai kawo sauki ga dillalan kayan gini a Sakkwato da makwabtanta Kebbi da Zamfara.

“Ina matukar farin cikin samun wannan sabon tsari na samar da babban shagon kayayyakin gini na Royal Edclusibe a Sakkwato saboda dalilai da yawa. Na farko, shi ne irinsa na farko a Sakkwato. Na biyu kuma an taimaka wa dillalai da abokan hulda wajen samar da kaya masu sauki da rage asara, domin yanzu ba sai mun yi tafiya mai nisa ba zuwa Kano ko Kaduna wajen samun wadannan kayayyaki,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Yanzu duk abubuwan da ake bukata mun samar da su cikin sauki. Mu muka samar da babban shagon ajiya sai Kamfanin WACL suka samar da kayayyakin.”

A jawabin, Manajan Tsare-tsare na Kamfanin WACL, Alhaji Abdulrahim Bello, wanda ya samu wakilcin Janar Manaja, Mista Bhaskar Rao cewa ya yi, “Hadakar ta tsakanin Ribalka Nig Ltd mun yi ne saboda burin da muke da shi na tabbatar da cewa mun tallafa wa bangaren gine-gine da samar da gideje masu sauki a Najeriya kuma masu karko da inganci da rahusa.”

Bello ya kara da cewa katafaren shagon kayayyakin zai taimaka wajen wayar da kan magina kan sanin kayan gini masu inganci.