✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kan Yarbawa ya rabu game da kisan ’yar jagoran Kungiyar Afenifere

Kashe Uwargida Funke Olakunri ’yar jagoran Kungiyar Kare Muradun Yarbawa ta Afenifere Mista Reuben Fasoranti ta bar baya da kura, inda wadansu manyan shugabannin Yarbawa…

Kashe Uwargida Funke Olakunri ’yar jagoran Kungiyar Kare Muradun Yarbawa ta Afenifere Mista Reuben Fasoranti ta bar baya da kura, inda wadansu manyan shugabannin Yarbawa da suka hada da ’yan siyasa da shugabannin kungiyoyi da sarkunana gargajiya suka samu sabani a tsakaninsu. Wadansu daga cikinsu suna sukar Gwamnatin Tarayya ce kan lamarin tare da yin zafafan kalamai ga al’ummar Fulani, har suke cewa za su dauki fansa a kan Fulani muddin aka ci gaba da yi musu irin wannan kisa yayin da wadansu suke cewa a yi taka-tsantsan a kan al’amarin kisan.

Kisan gillar da wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, wadansu sun dora kisan a kan Fulani makiyaya wanda ya faru a hanyar Akure zuwa Ore a Jihar Ondo a ranar Juma’a da ta gabata.

Basaraken gargajiya Ooni na Ife Cif Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya yi barazana game da hadin kan kasa muddin aka ci gaba da samun irin wannan kisan gillar a yankinsu. Oba ya ce “A hanzarta daukar matakin shawo kan irin wannan kisan rayuka da dakile ayyukan fashi da makami tun kafin al’amarin ya kazance domin aiki ne da ya rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya. Irin abubuwan da suke faruwa yanzu a kan tabarbarewar tsaro a kasar Yarbawa idan Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomi suka kasa shawo kansa to zai iya tilasta mutanenmu daukar matakin da ba zai yi kyau ga hadin kan Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa ba,” inji Basaraken na Ife.

Shi kuwa Shugaban Kungiyar OPC Cif Gani Adams cewa ya yi kada a ga laifinsu idan suka dauki mataki, “Muna so duniya ta sa ido ta kalli abubuwan da ake yi wa mutanenmu a yanzu domin kada a ga laifinmu idan muka mayar da martani,” inji shi.

Shi kuwa Tsohon Gwamnan Jihar Ogun Otunba Gbenga Daniel cewa ya yi irin wannan kisan gillar ka iya sa mutanensu su dauki fansa “Akwai hadarin gaske ga ci gaba da aukuwar irin wannan al’amari wanda zai iya tilasta mutanenmu daukar matakin kare kansu idan gwamnati ta kasa shawo kan wannan barna da ake yi mana,” inji shi.

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo cewa ya yi kisan Uwargida Funke Olakunri alama ce ta koma bayan Najeriya. Ya ce “Zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira da kakkausan harshe ga dukkan bangarorin gwamnati su yi duk abin da suke iyawa wajen gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki. Dole ne mu hada kai tare domin shawo kan matsalar tsaro musamman miyagun ayyukan fashi da makami da satar mutane da kisan mutane da ake zargin Fulani da aikatawa.”

Sai dai Jagoran  Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ne ga ’yan Najeriya su daina dora laifin abubuwan da ke faruwa a kan wata kabila ita kadai kuma kada su bari matsalar kashe-kashen rayuka ta raba su.

Ya yi wannan kira ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da ya ziyarci gidan Jagoran Kungiyar Afenifere Cif Reuben Fasoranti domin yi masa ta’aziyar rasuwar ’yarsa ’yan bindigar suka kashe.

Sanata Bola Tinubu wanda yake tare da tsohon Gwamnan Jihar Osun Cif Bisi Akande da Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya yi kiran cewa kada a kuskura a bari wannan al’amari ya kai ga raba Najeriya. Ya ce kamata ya yi hakan ya zama hanyar samo mafita a kan matsalar tsaro da ke yi wa kasar nan barazana. “Miyagun ayyuka da suka hada da kisan kai da fashi da makami da satar mutane da fyade an dade ana aikata su wanda bai kamata a dora laifin aukuwarsu ga wata kabila ita kadai ba,” inji shi.

Bayan nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro, ya ce “Idan muka duba kundin tarihin satar mutane da garkuwa da su a Najeriya, muna da masaniyar inda aka faro ta da yadda aka faro.” Ya yi tambayar cewa “Kasurgumin mai satar mutanen nan mai suna Ebans da aka kama shin  Bafulatani ne? Matsalolin da suke yi wa tsaron kasa barazana suna matukar bukatar karin ’yan sanda da ya kamata su samu horo da za a tura su sassa daban-daban na kasar nan domin yakar miyagun ayyuka.”

Da yake magana a kan kisan da aka yi wa Uwargida Funke Olakunri Sanata Tinubu cewa ya yi wannan abin bakin ciki ne kwarai sai dai babu wanda zai iya dawo da ita domin ta amsa kiran Mahallici ne. Ya ce “Marigayiya Funke ta kusance ni kwarai domin kwana 5 kafin rasuwarta muka yi wata ganawa muka tattauna a kan matsalar koshin lafiyar mahaifinta.” Ya yi addu’ar kada Allah Ya sa a sake ganin irin haka a nan gaba.

Sai dai Kungiyar Afenifere ta soki kalaman Sanata Bola Tinubu na cewa bai kamata ’yan Najeriya su rika dora alhakin aukuwar irin wadannan kashe-kashe a kan wata kabila ita kadai ba.

Kungiyar ta ce ba ta dauki Sanata Tinubu a matsayin daya daga cikin masu fafutikar kare muradun Yarbawa ba domin ya ki cewa komai a kan barnar da Fulani makiyaya suke yi wanda hakan ke nuna cewa yana daya daga cikin magoya bayansu.

Kakakin Kungiyar Afenifere, Mista Yinka Odumakin  ya fitar da wata sanarwa wacce yake bayyana, kiran da Tinubu ya yi ga ’yan Najeriya a garin Ondo a ranar Lahadi cewa su daina dora wa Fualni makiyaya laifin satar mutane da garkuwa da su su kadai, da cewa hakan ya nuna cewa yana goyon bayan ta’asar da makiyayan suke yi a kasar ke nan. “Yana goyon bayansu domin a cikin watan Oktoban bara a Abuja shi ya fara kawo shawara a kan batun RUGA cewa a bayar da dukkan filayen da ke cikin dazukan da ba a amfani da su ga makiyaya. Yau kuma a garin Ondo da ya zo ta’aziya ga Fasoranti bayan ya kammala sai ya koma yana yin bayanai kamar ya je ya yi rawar murna a kabarin marigayiyar ne inda yake cewa jama’a su daina kallon Fulani makiyaya a matsayin masu satar mutane da garkuwa da su domin ba makiyaya ne suka fara satar mutane ba,” inji Odumakin.

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin bincikowa tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan kisan gilla.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda ya zanta da Cif Reuben Fasoranti ta tarho ya jajanta wa Jagoran na Kungiyar Afenifere da rokon Allah Ya sanya masa hakurin wannan rashi.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa sassan tsaro na kasar nan sun fara gudanar da ayyuka don zakulo dukkan wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Bayanin haka yana kunshe ne cikin takardar sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina, ya sanya wa hannu inda ya ce Cif Reuben Fasoranti ya nuna matukar farin ciki da godiya ga Shugaba Buhari a kan girmamawar da ya yi masa tare da iyalinsa a kan wannan babban rashi da suka yi. Cif Fasoranti ya yi addu’ar Allah Ya samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Aminiya ta  tuntubi Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Jihar Ondo Alhaji Bello Garba, wanda ya yi bayani a kan kisan gillar da ya faru da kuma yadda suke ganin al’amarin musamman ganin yadda ake danganta kisan ga Fulani makiyaya.

Alhaji Bello ya ce “A madadin al’ummar Fulani da ke Jihar Ondo ina mika ta’aziyya ga Jagoran Kungiyar Afenifere da iyalinsa. A daidai wannan lokaci kuma muke nuna bakin cikinmu a kan yadda ake yi mana mummunar fassara ana danganta mu da aikata miyagun ayyuka. Wallahi ba a yi mana adalci da wannan fassara ba domin Kungiyar Miyetti Allah a Jihar Ondo tana yin aiki kafada-da-kafada da mahukunta da jami’an tsaro inda Gwamnan Jihar Ondo Mista Rotimi Akeredolu yana sane da irin hadin kan da Fulani suke bayarwa kan samo hanyar dakile miyagun ayyuka. Akwai Kungiyar Sintiri da muka kafa da take aikin hadin gwiwa da jami’an tsaro a ko’ina a jihar kuma mahukunta sun yaba mana kan ayyukan da muke yi. Amma abin bakin ciki sai a rika amfani da kabilanci wajen bata mana suna ana danganta Fulani da aikata miyagun ayyuka. Wannan ba daidai ba ne kuma babu adalci da domin ana kashe mana mutane da yin garkuwa da su da sace mana shanu amma ba mu taba jin an ce Yarbawa suna kashe Fulani ba.”

Da yake zantawa da ’yan jarida Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ondo Mista Undie Adie ya ce zai yi wuyar gaske a yanzu a ce Fulani makiyaya ne suka aikata wannan danyen aiki. Kuma ya bayar da tabbacin cewa rundunarsa za ta yi duk abin da take iyawa wajen gano  wadanda ke da hannu wajen kisan Uwargida Funke Olakunri.

Jama’a dai suna tambaya me ya sa sauran rayukan ’yan Najeriya da ake kashewa a Benuwai da Katsina da Kaduna da Zamfara da Filato da Kudu maso Kudu da sauran yankunan Najeriya wadancan shugabannni na Yarbawa ba sa daga jijiyoyin wuya  sai idan ya taba ’yan yankinsu?