Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kananan hukumomi da yankunan raya kasa sun sa zare a Nasawara kan kason kudi

Matakin da Gwamnatin Tarayya ta  dauka na bai wa kananan hukumomi kudadensu kai-tsaye ya tada kura a wasu kananan hukumomin jihohin Jihar Nasarawa inda ta kai ana samu takaddama a tsakanin gudumomin raya kasa da kananan hukumomin, inda hakan yake jawo jinkiri wajen biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomin.

Bayan jinkiri da lamarin ya jawo akwai kuma rashin cimma yarjejeniya kan tsarin raba kudade a tsakanin kananan hukumomin da gundumomin raya kasa a jihar wanda hakan ke barazanar jefa Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule a tsaka-mai-wuya.

ADVERTISEMENT

Hakan ya biyo bayan wani zargi da ake yi wa shugabannin kananan hukumomin jihar 13 ne cewa sun ki amincewa su raba kasonsu da Gwamnatin Tarayya ta bayar da gundumomin raya kasa 18 da ke karkashinsu, gundumomin da tsofaffin gwamnonin jihar Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Umaru Tanko Al-Makura suka kirkiro don saukake harkokin gwamnati.

Kirkkro gundumomin raya kasa wata yarjejeniyar ce ta cikin-gida ta gwamnatin jihar, kuma binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa akwai wani shiri na musamman da ake yi da dadewa a jihar inda ake raba kudaden kananan hukumomin a tsakaninsu da gundumomin raya kasa duk da cewa Gwamnatin Tarayya ba ta amince da irin wadannan gundumomi ba. Wannan ya sa  da Gwamnatin Tarayya ta soma bai wa kananan hukumomin kudadensu kai-tsaye sai suka ki amincewa su ci gaba da raba kudaden da gundumomin saboda a cewarsu idan suka  ci gaba da yin haka ba za su iya biyan albashi da sauran hakkokin ma’aikatansu ba musamman ganin ma’aikatan gundumomin raya kasar sun fi ma’aikatansu yawa sakamakon rashin tsari da adalci a harkokinsu.

ADVERTISEMENT

Akwai kuma zargin da ake yi cewa wadansu manyan ’yan siyasa da  masu rike da manyan mukamai a kananan hukumomin suna hada baki don yin awon gaba da dukiyar kananan hukumomin ta hanyar saka sunayen ’yan uwansu da wadanda suka mutu a jerin sunayen wadanda ke karbar albashi.

Misali a Karamar Hukumar Lafiya wacce ta kunshi gundumomin raya kasa na Lafiya ta Kudu da Lafiya ta Arewa, binciken wakilinmu ya gano cewa ma’aikatan gundumomin raya kasar biyu, sun fi wadanda ke ainihin Karamar Hukumar Lafiya yawa. Haka lamarin yake a kusan dukkan kananan hukumomin inda duk da dakatarwa tare da tilasta ma’aikatan da suka cancanci ritaya yin haka a kowacce shekara ana ci gaba da samun karin ma’aikata. Misali a Karamar Hukumar Obi da ta kunshi yankunan raya kasa na Jankwe da Daddere an tsara cewa za a bai wa Karamar Hukumar Obi kashi 40 cikin 100 na kasonta na watan Yunin bana, yayin da yankunan  raya kasa biyu za su samu kashi 30 cikin kowannensu. Amma a yanzu ana zargin cewa Yankin  Raya Kasa na Jankwe ya ki amincewa da tsarin saboda a cewarsa idan aka yi haka ba a yi masa adalci ba, saboda yanki na da mazabu 5 ne ya yin da Daddere ke da guda daya kacal. Kuma ma’aikatansa sun fi na Karamar Hukumar Obi kanta yawa.

Lokacin da wakilinmu ya tuntube shi don jin ta bakinsa a kan lamarin mai taimaka wa Gwamnan Jihar na Musamman a kan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautun Mista John Mamman ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar ta tsara wani kwamiti da ya kunshi dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar da zai nuna musu yadda za su raba kudin a tsakaninsu da yankunan raya kasa. Haka kuma a cewarsa an tsara yadda za a rika biyan sarakunan gargajiya na jihar da sauran wadanda ke amfana a asusun kananan hukumomin hakkokinsu.

Ya ce “A zaman kwamitin mun tsara yadda za a rika raba kudaden a tsakanin kananan hukumomin da gundumomin raya kasa. Dole ne a tafi da wadannan gundumomin raya kasa duk da cewa Gwamnatin Tarayya ba ta san da su ba, amma kada ka manta an kirkiro su ne bisa dokar Majalisar Dokokin Jihar nan. Saboda haka su ma suna cikin doka.”

Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON) reshen jihar kuma Shugaban Karamar Hukumar Lafiya, Alhaji Mu’azu Maifata ya ki yin bayyani game da batun a lokacin da wakilinmu ya tuntubeshi

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Alhaji Ibrahim Balarabe ya nuna takaicinsa game da yadda harkokin kananan hukumomin suke tafiya, inda ya kafa wani kwamiti don gudanar da bincike kan rashin biyan albashin watan Yuni ga ma’aikatansu da kuma cire musu wasu kudade daga albashinsu ba bisa ka’ida ba.

Kuma rahoton da kwamitin ya gabatar ga majalisar ya bayyana cewa ya gano wasu kura-kurai da dama a harkokin kananan hukumomin da suka hada da saka sunayen wadansu da suka mutu da wadanda suka yi ritaya da wdanasu da dama da ba a san da su ba, da karin girma ba bisa ka’ida ba da sauransu.

Kwamitin ya kuma gano cewa a yanzu kananan hukumomin jihar 4 ne kacal da suka hada da Keffi da Awe da Wamba da Keana daga cikin 13 za su iya biyan cikakken albashin ma’aikatansu.