✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kananan Hukumomi shida da adadin masu Coronavirus a Legas

A ranar Juma’a 3 ga watan Afrilu ne Kwamishinan lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi, ya fitar da jerin adadin wadanda suka kamu da…

A ranar Juma’a 3 ga watan Afrilu ne Kwamishinan lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi, ya fitar da jerin adadin wadanda suka kamu da Coronavirus a Legas daga kananan hukumomin shida a jihar.

Karamar hukumar Eti-Osa, ita tafi yawan mutanen da suka kamu da adadin mutum 47, sai karamar hukumar Ikeja babban birnin jihar da ke biye mata da adadin mutum 24, sai karamar hukumar cikin garin Legas wato Lagos Mainland da tazo na uku a jerin da mutum 14.

Jerin kananan hukumomin da aka samu bullar cutar a Legas sun hada da:

1) Eti-Osa – 47

2) Ikeja – 24

3) Lagos Mainland – 11

4) Alimosho – 1

5) Agege – 1

6) Ikorodu – 1

Wannan ya nuna cewa akwai ragowar kananan hukumomi 31 da ba a kai ga tabbatar da ko wani ya kamu da cutar ba.

Farfesa Abayomi, ya ce a jihar Legas an tabbatar da adadin mutum 98 da suka kamu da cutar daga kananan hukumomi shida, an kuma sallami mutum 24 daga cikinsu, inda kawo yanzu ake da mutum 74 da ke dauke da cutar.

Ya kara da cewa, mafi yawan wadanda ke dauke da cutar masu shekaru 30 zuwa 59 ne, sai mutum uku kacal da ke da shekaru 60 zuwa 70, kana kashi 64 cikin 100 na masu cutar a Legas maza ne, yayin da ake da kaso 36 cikin 100 na mata a cikinsu.