Daily Trust Aminiya - ‘Kananan hukumomin da za a yi ambaliyar ruwa’
Subscribe

‘Kananan hukumomin da za a yi ambaliyar ruwa’

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce kimanin kananan hukumomi takwas a jihar Sakkwato ne cikin hatsarin fuskantar ambaliyar ruwa.

Babban daraktan hukumar, AVM Muhammadu Mohammed shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ayarinsa ya kai wa bataliyar sojonjin Najeriya ta 26 da ke barikin sojoji na Giginya a Sakkwato.

A cewarsa, kanana hukumomin sun hada da Goronyo, Sakkwato ta Arewa, Sabon Birni, Rabah, Isa, Sakkwato ta Kudu, Dange-Shuni, Kware da kuma Wurno.

Babban daraktan wanda ya samu wakilcin daraktan ayyuka na musamman Joseph Akujobi, ya ce yawan samun ambaliyar da ake a jihar na barazanar ga harkar samar da abinci.

Ya kuma ce, “Mun zo nan ne domin ziyarar wayar da kai a kan ambaliyar shekara ta 2020.  An san Jihar Sakkwato a matsayin daya daga cikin manyan masu noma kayan abinci a Najeriya, amma yawan barazanar ambaliyar da ake samu a jihar a bana na barazana ga hakan.

“Ambaliya ta zama wata annoba da ke faruwa kusan duk shekara. Bayan mummunar da aka shaida a shekarar 2012, an samu makamanciyarta a 2018 wacce ta kai ga ayyana dokar ta-baci a jihohi da dama”, inji shi.

Mohammed ya yi kira ga masu hannu da shuni da su bullo da managartan tsare-tsare da za su taimaka wajen fadakar da jama’a da kuma gargadi a kan lokaci musamman in akwai hasashen samun ambaliyar.

Da yake mayar da martani, kwamandan bataliyar ta 26, Laftanar Kanar Usman Mohammed ya ce rundunar sojin tana da sashe na musamman da ke kula da bala’o’i saboda da shirin ko ta kwana irin na ambaliya.

texem
More Stories