✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kananan manoman Arewa ba su samun tallafin gwamnati – Pambeguwa

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Hatsi ta Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Ahmad Pambeguwa ya koka cewa akasarin kananan manoman Arewacin kasar nan ba su amfana…

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Hatsi ta Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Ahmad Pambeguwa ya koka cewa akasarin kananan manoman Arewacin kasar nan ba su amfana da  tallafin da Gwamnatin Tarayya ke bai wa manoma.

Pambeguwa ya ce hakan na faruwa ne duk  da cewa al’ummar Arewa da manoman sun amsa kiran da gwamnatin ta yi na jama’a su koma noma amma har yanzu ba su samu tallafi ba.

Ya bayyana hakan ne a zantawarsa da Aminya inda ya ce mafi yawan kananan manoman ba su ma san ana bada tallafin ba ballantana su samu.

Sai ya yi kira ga gwamnatin da ta samar da tsarin da za ta rika sayen kayan amfanin noma kai-tsaye a wajen kananan manomar kasar nan.

“Muna kara kira ga gwamnati cewa mutane sun amsa kira na komawa gona da yadda ake tura masana su rika zuwa suna fadakar da mutane yadda za a samu ci gaba a fannin noma.

“Sai dai fa batun tallafi da gwamnati ke bayarwa har yanzu muna kara sanar da cewa ba ya zuwa hannun kananan manoma. Domin ba su ma san da ana bada tallafin ba. Haka kuma batun sayen kayan amfanin gona a hannun manoma shi ma wadnsu mutane ne kawai ke samun wannan dama domin wasunsu ba su da alaka da noma don haka a gyara,” inji shi.

Ya kara da cewa fito da wani tsarin sayen kayan amfanin noma kai-tsaye daga hannun manoma, musamman kananan manoma  zai taimaka musu kuma zai inganta harkar noma a kasar nan.