✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Kotu ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Ganduje

Kotun da ke sauraron kararrakin zaben ‘yan takarar Gwamnan jihar Kano da ke Kano, wanda aka shigar game da zaben watan Maris na 2019, ta…

Kotun da ke sauraron kararrakin zaben ‘yan takarar Gwamnan jihar Kano da ke Kano, wanda aka shigar game da zaben watan Maris na 2019, ta ce Gwamna Umar Abdullahi ne zababben gwamnan jihar Kano a zaben da aka gudanar ranar 23 ga watan Maris 2019.

Kotun ta kori karar jam’iyyar PDP da dan takarar jam’iyyar, Abba Kabir Yusuf, inda yake kalubalantar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC da yin magudin zaben da aka yi.

Mai shari’ar Halima Shamaki Muhammad, ce ta yanke wannan hukunci a yau Laraba.