✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Pillars ta karbi kofin gasar Premier

A jiya Alhamis ne ake sa ran kulob din Kano Pillars da ke Kano da ake wa lakabi da “Sai Masu Gida” ya karbi kofin…

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar KanoA jiya Alhamis ne ake sa ran kulob din Kano Pillars da ke Kano da ake wa lakabi da “Sai Masu Gida” ya karbi kofin gasar rukunin Premier na Najeriya da ya lashe tun a watan jiya.
Sau biyu kenan Pillars ke lashe kofin a jere da hakan ya sa ta kafa sabon tarihi a Najeriya.
Sai dai kulob din ya sake fafatawa a gasar cin kofin Charity a tsakaninsa da na Enyimba da ke Aba a jiya Alhamis a garin Warri.  Idan Pillars ta samu nasara kenan ta za hada kofuna biyu a kakar wasa ta bana, kamar yadda ita ma Enyimba za ta hada kofuna biyu idan ta samu nasara..
Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ce ta sanya kofin don fafatawa a tsakanin kulob din biyu watau wacce ta lashe gasar rukunin Premier da kuma wacce ta lashe kofin kalubale na kasa da aka fi sani da Confederations Cup.
Shugaban kulob din Pillars Alhaji Abba Yola tuni ya tabbatar da labarin cewa Hukumar NFF za ta ba kulob din kofin Premier da ta lashe a watan jiya a garin Owerri da zarar an kammala wasan cin kofin Charity a tsakaninsu da kulob din Enyimba na Aba.