✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Pillars ta sallami ’yan kwallo 6

Rahotannin da ke fitowa daga kulob din Kano Pillars sun nuna kulob din ya sallami  ’yan kwallo 6 da bai sabunta musu kwantaragi ba.  Kwantaraginsu…

Rahotannin da ke fitowa daga kulob din Kano Pillars sun nuna kulob din ya sallami  ’yan kwallo 6 da bai sabunta musu kwantaragi ba.  Kwantaraginsu dai ta kare ne da kulob din a kakar wasan da ta wuce yayin da ake gab da fara kaka ta bana, kuma kulob din ya nuna ba ya bukatarsu.

Kamar yadda kulob din ya sanar a shafin sadarwarsa na Intanet a shekaranjiya Laraba, ’yan kwallon da aka sallama sun hada da  Seun Akinyemi da Shammah Tanze da Kalam Sikiru da sauransu.

Sanarwar ta ce kulob din ya sayi sababbin ’yan wasa daga kulob daban-daban da suka hada da Abdullahi Musa daga Wikki Tourists da ke Bauci da Nasiru Sani daga kulob din Enyimba da kuma Stone Samuel daga kulob din Go Round.

Kulob din ya ce ya yi wannan gyara ne a yunkurinsa na tunkarar kakar wasa ta bana da kuma fuskantar gasar cin Kofin Kalubale na Afirka da Pillars za ta wakilci kasar nan bayan ta lashe Kofin Kalubale na Kasa inda ta lallasa Neja Tornadoe da ci 4-3 a bugun finareti.